An gudanar da taron baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na CIIE karo na 6 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, daga ranar 5 zuwa 10 ga watan nan da muke ciki.
A ranar 5 ga wannan wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sakon taya murna ga taron, inda ya yi nuni da cewa, an yi nasarar shirya taron sau biyar tun daga shekarar 2018, lamarin da ya taimaka matuka wajen kafa sabon tsarin ci gaban duniya, da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Haka kuma Xi ya jaddada cewa, har yanzu ba a kai ga farfado da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata ba, don haka akwai bukatar kasashen duniya daban daban su hada kai tare, da yin hadin gwiwa a tsakaninsu domin samun ci gaba tare. Kaza lika a ko da yaushe, kasar Sin tana samar da damammaki ga sauran kasashen duniya, ta hanyar bude kofarta ga ketare.
- Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya
- Sin Na Adawa Da Kutse Ta Intanet
Kana kuma, firayinministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude taron a ranar 5 ga wata, tare da gabatar da muhimmin jawabi, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya domin samun ci gaba tare.
Baki daga kasashe, yankuna, da hukumomin kasa da kasa guda 154, da kamfanoni fiye da 3400 na duniya sun halarci taron, ciki har da kamfanoni masu alaka da raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” sama da 1500. Abin da ya kamata a lura da shi, shi ne a cikin wadannan kamfanoni fiye da 3400, wasu da dama sun halarci taron na CIIE sau 6 baki daya.
Taron baje kolin CIIE karo na 6 da aka gudanar a Shanghai, ya samu yabo daga jagororin kasashen duniya, da jami’ai daga sassa da dama, wadanda suka jinjinawa gudummawarsa, a matsayin dandali dake samar da tarin damammaki ga ’yan kasuwa, da kamfanonin duniya baki daya. Kaza lika sun yaba da yadda taron baje kolin ke taka rawar gani, wajen yaukaka hadin gwiwar cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa, tare da ingiza hadin gwiwar tattalin arziki da ci gaban duniya gaba daya.
Mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Paul Mashatile, ya jinjinawa kasar Sin bisa yadda take kara bude kofofin kasuwanninta ga duniya, musamman ma ga kasashen Afirka. A cewarsa, taron baje kolin CIIE ya samarwa kamfanonin duniya wata dama ta baje hajoji da hidimominsu, tare da zarafin fadada cudanya da abokan hulda.
A nata tsokaci kuwa, babbar sakatariyar taron MDD game da cinikayya da samar da ci gaba Rebeca Grynspan, cewa ta yi CIIE ya shaida kudurin kasar Sin na daidaita alakar cinikayya da sauran sassan duniya. Ta kara da cewa, baya ga kawar da shingen cinikayya ko karfafa zuba jari, kasar Sin ta kuma shaidawa duniya aniyarta ta gabatarwa duniya sabbin dabarun samar da ci gaba da musayar al’adu.
Shugaban kungiyar masu harkokin kasuwanci ta na’urorin zamani ta Sin da Turai dake Brussels, Luigi Gambardella, ya ce taron baje kolin CIIE, gayyata ce ga kasashen duniya, don su ci gajiyar damammakin kasuwar kasar Sin, tare da hada hannu tare domin samun moriyar juna. A cewarsa, CIIE alama ce bayyananniya cewa, kasar Sin na mara baya ga dunkulewar tattalin arzikin duniya, kuma a shirye take ta bude kofar kasuwarta ga duniya. Ya ce, taron baje kolin CIIE na da muhimmin tasiri kan tattalin arziki, kuma zai bayar da gudunmuwa ga habaka harkokin cinikayya na kasar Sin, da bunkasa cinikayya a duniya, a lokacin da ake matukar bukatar hakan.
Ya kuma yaba da yadda aka samar da wani dandalin hadaka na musammam, ta hanyar tattara shugabannin kasuwanci, da jami’an gwamnatoci, da masana sana’o’i daga fadin duniya a wuri guda. Yana mai cewa, irin wannan hadaka za ta iya haifar da sabbin damarmakin kasuwanci da hadin gwiwa. Har ila yau, Gambardella yana ganin bikin na CIIE a matsayin dandalin kaddamar da sabbin kirkire-kirkire, kamar sabbin mutum-mutumin inji, da ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi kamar na lantarki, da sabbin nasarorin da aka samu a fannin kirkirarriyar basira ta AI. Yana mai cewa, wadannan fasahohi za su bunkasa sana’o’i, tare da shawo kan kalubalen duniya.
Taron baje kolin na CIIE, wani bangare ne na manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen ketare, da tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, da kokarin maida ci gaban kasar ya zama wata dama ta raya tattalin arzikin duniya.
A matsayinsa na taron baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa wata kasa na farko a duniya, bikin na CIIE ya kasance wani muhimmin dandali na saye da sayarwa na kasa da kasa, da inganta zuba jari, da musaya tsakanin al’ummomi da na al’adu, da hadin gwiwar dake shafar kowa da kowa, tun lokacin da aka fara gudanar da shi a shekarar 2018.
A taron CIIE karo na farko da aka gudanar a watan Nuwamban shekarar 2018, kasar Sin ta yi alkawarin cewa, za ta shirya taron a ko wace shekara, tare da samun kyakkyawan sakamako bisa babban mataki. Kamar yadda ta sha bayyanawa, Sin tana ingiza burin dukkan kasashen duniya na cin gajiya daga damammakin babbar kasuwar kasar, da moriyar dake tattare da kara bude kofar kasar, da zurfafa hadin gwiwar sassan kasa da kasa. Don haka, manufar kasar Sin ta bude kofa, ba kasar kadai za ta amfana ba, har ma da ragowar kasashen duniya baki daya.
Alkaluma na nuna cewa, yayin tarukan CIIE guda 5 da aka gudanar a baya, kasashe da hukumomin kasa da kasa 131 ne suka nuna kayayyaki, da al’adu da dai sauransu a taron na CIIE, kana an gwada sabbin kayayyaki, da sabbin fasahohi, da sabbin hidimomi fiye da dubu 2, wadanda suka kasance irinsu na zamani matuka, kuma yawan darajar kwangilolin da aka kulla ta kai dalar Amurka biliyan 350.
A ’yan shekaru da dama da suka wuce, karin kasashen duniya, da ma kamfanoninsu, suna halartar taron baje kolin CIIE, lamarin da ya nuna cewa, yayin da wasu ke yunkurin yada ra’ayi na kashin kai, da kuma ba da kariya kan cinikayya, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan hada hannu tare, domin samun moriyar juna da nasara tare. Babu wanda zai iya dakile haka, saboda wannan shi ne burin kasashen duniya.
Kasashen duniya suna cin gajiyar taron baje kolin CIIE sosai. Muddin wani kamfani ya baje kayayyakinsa a taron baje kolin CIIE, to, zai samu damar sayar da kayayyakinsa a kasuwar kasar Sin, tare da samun mabudin kasuwar kasar Sin da na wurin ajiyar dukiyoyi.
A idanun kamfanoni masu jarin waje, halartar taron na CIIE ya ba su damar samun bunkasuwa. Kayayyakin da suke baje kolin su a taron CIIE, sun zama hajojin da suke sayarwa a kasar Sin, kana suna zuba jari a kasar Sin a maimakon halartar taron na CIIE kadai. Tun tuni kasar Sin ta yi alkawarin mayar da kasuwar Sin zuwa kasuwar duniya mai kunshe da kowa. Ta kuma cika alkawarinta a zahiri. Ta yi ta ba kamfanonin kasa da kasa damarmakin samun ci gaba.
Alkaluman tattalin arzikin kasar Sin na watanni 9 na farkon bana kuma sun karfafa gwiwar kamfanonin masu jarin waje. Karuwar tattalin arzikin kasar Sin wato GDP ta kai kaso 5.2 a watanni 9 na farkon bana bisa makamancin lokaci na shekarar bara, karuwar da ta fi ta rukunonin duniya masu karfin tattalin arziki. Ciki kuma, karuwar yin sayayya ta fi jan hankali, wadda ta taimakawa karuwar GDP da har kaso 4.4. Wadannan alkaluma sun samar wa kamfanoni masu jarin waje kyawawan damarmaki.
Baya ga dimbin al’umma da suka kai biliyan 1.4, da kuma masu matsakaitan kudin shiga sama da miliyan 400, gwamnatin kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan bude kofa ga kasashen ketare, lamarin da ya jawo hankalin kamfanoni masu jarin waje da dama, musamman ma shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ke kokarin aiwatarwa cikin hadin gwiwar kasa da kasa, wadda ke amfanar kasashen duniya sosai.
A sashen nune-nunen kasa da kasa a taron CIIE na wannan karo, akwai kasashe 64 da suke raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” daga cikin dukkan kasashen 72. A ’yan kwanakin baya, jiragen kasa dake tafiya tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, suna ta jigilar kayayyakin kasashen dake raya shawarar zuwa taron CIIE.
Har ila yau, taron na CIIE na bai wa daukacin kasashen duniya damar samun ci gaba, musamman ma ta hanyar taimakawa kasashe masu rauni samun bunkasuwa, lamarin da ya burge wasu kamfanoni. Kasashe mafiya karancin ci gaba, wadanda suke raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, sun samu wurin nune-nune ba tare da biyan kudi ba a taron na CIIE, tare da samun kudin tallafin yin nune-nune, da harajin gata kan kayayyakin da za su nuna, ta yadda kayayyakinsu masu halin musamman za su samu damar shiga kasuwar kasar Sin.
Kokarin da kasar Sin take bayarwa ya shaida cewa, manufar shirya taron na CIIE ita ce kara azama kan gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkan bil Adama. Taron na CIIE ya sanya kasashen duniya sun kara sanin aniyar kasar Sin ta bin manufar cudanyar sassa daban daban, da samar wa kasashen duniya damar ci gaba, da kuma matakan da take dauka.
Tuni dai wasu daga kasashen yamma suka shelanta cewa, masu jarin waje suna janyewa daga kasar Sin, amma yadda kamfanoni masu jarin waje suke halartar taron CIIE sau da dama, ya sa gaskiya za ta yi halin ta.
Hukumar kara azama kan cinikayya ta kasar Sin, ta kaddamar da rahoto a kwanan baya, wanda ke cewa kamfanoni masu jarin waje da aka yi musu tambaya, wadanda yawansu ya wuce kaso 80, sun gamsu da yanayin kasuwancin kasar Sin. Bugu da kari, ya zuwa yanzu kasuwar kasar Sin na jan hankalinsu sosai. Taron CIIE karo na 6, ya kara nuna yadda ake amfani da damar da kasar Sin ke samarwa.
(Mai fassarawa: Tasallah Yuan daga CMG Hausa)