Wasu lauyoyi masu da’awar kishin al’ummar Jamhuriyar Nijar sun shigar da kara a kotun ECOWAS a Abuja don bukatar haramta takunkumi kan talakawan Nijar.
ECOWAS dai ta saka takunkumi kan Nijar biyo bayan juyin mulkin soji da su ka kifar da gwamnatin Muhammad Bazoum.
- Labarin Rasuwar Janar CG Musa Ba Gaskiya Ba Ne – Rundunar Tsaron Nijeriya
- Guterres Ya Jinjinawa Sin Game Da Shirya Muhawara Kan Tasirin Samar Da Ci Gaba Mai Dorewa
Lauyoyin, wadanda ba su amince gwamnatin sojin Nijar ta Janar Abdulrahman Tciani ce ta turo su ba, sun ce sam ba daidai ba ne ana tuhumar sojoji da laifi, a hada har da al’ummar Nijar.
Metri Ahmed Mammane na wakiktar wasu mutum bakwai masu son a janye takunkumi kan Nijar ya ce yana da kyau a duba hakkin fararen hular Nijar da rufe kan iyaka ya jefa rayuwarsu cikin garari.
Shi ma lauya Metri Isma’il Tambo Mousa, ya ce al’ummar Nijar na cikin mawuyacin yanayi don haka kotun ta tilasta wa ECOWAS ta janye takunkumin in ya so ta san hanyar da za ta dauki mataki kan masu juyin mulki.
Kotun ta dage zaman batun zuwa ranar 7 ga watan DIsamba don yanke hukunci.
Jami’an tsohuwar gwamnatin Nijar irin su Dokta Manzo Abubakar sun sha nanata bukatar dawo da ragama hannun farar hula ko kuma shugaba Bazoum don samun sulhu mai dorewa.
Da alamu ECOWAS na son amfani da takunkumin wajen horar da sojojin juyin mulki a madadin matakan sojin.