A daidai lokacin da matsalar tsaro ta addabi wuraren da ake hakar ma’adanai a yankin Afirika ta yamma, masu ruwa da tsaki a karkashin jagorancin kungiyar ‘Global Rights Nigeria’ da ‘African Coalition for Corporate Accountability’ sun nemi Nijeriya da sauran kasashen kungiyar ECOWAS su tabbatar da samar da tsaro ga al’ummun da ake hakar ma’adanai a yankinsu don suma su ci gajiyar ma’adanan da ake hakowa.
Wannan na daya daga cikin matakan da kungiyar ta dauka bayan taronta na kwana 3 a Abuja Nijeriya, an dai gudanar da taron ne daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Nuwamba 2023.
- Gwamna Nasir Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Naira Biliyan 250 Ga Majalisar Dokokin Kebbi
- Majalisar Dokokin Kaduna Ta Dakatar Da Kansiloli 8, Ta Karɓe Ragamar Majalisar Kagarko
Taron ya samu halartar kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da kasashen waje da kuma wakilai daga kasashe kamar su Ghana, Mali, Coted’Iboire, Guinea, Sierra Leone, Kenya, da kuma ‘Democratic Republic of Congo, Zambia, Uganda, da kuma kasar Afirka ta kudu.