ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Samar Da Ci Gaba A Bangaren Ma’adinai: Ministan Yaɗa Labarai Ya Yaba Da Koƙarin Takwaransa Na Ma’adinai

by Sulaiman
2 years ago
Ma'adinai

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa takwaransa na Ma’adinai kan abin da ya kira “manyan matakan cigaba da ake samu a Ma’aikatar Ma’adinai da ake ɗauka don kawo sauyi a bangaren a matsayinsa na wanda ke sahun gaba na muradun tattalin arzikin Nijeriya.”

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya fitar ta ce,  Idris ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ga Ministan Ma’adinai, Mista Henry Dele Alake, a ranar Alhamis a Abuja.

  • Bayan Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, Gwamna Uba Sani Ya Nemi Haɗa Hannu Da ‘Yan Adawa
  • NPA Ta Gargadi Masu Jibge Kwantaina Ba Bisa Ka’ida Ba

Ministan ya yi la’akari cikin gamsuwa da cewa ayyuka masu tasiri a fagen ma’adinai waɗanda ke bada sakamako a kyakkyawan sauye-sauye da ake matuƙar buƙatar su da canza muradu, wanda ya yi daidai da manyan manufofin Renewed Hope Agenda ta gwamnatin Tinubu.

ADVERTISEMENT

A cewar Idris, Mista Alake ya na dasa ginshiƙan gudanarwa waɗanda ba a saba ganin irin su ba a sashen ma’adinai sannan su na haifar da kyakkyawar fata a zuciyar ‘yan Nijeriya game da gina ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki.

Ya bayyana ziyarar tasa ga Alake a matsayin ziyarar aiki ta farko da ya kai wa wani takwaran sa minista, ya na faɗin cewa Alake mutum ne wanda ya samu sani daga sassa daban-daban, kuma mai basirar cimma nasara a wani sashe da ya kusa durƙushewa, wanda zai ƙarfafa hanyoyin kuɗin shiga na Nijeriya ya kuma faɗaɗa damar ɗaukar ma’aikata.

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

Shi kuma Mista Alake sai ya ce shi da Idris sun daɗe su na hulɗar siyasa tare, kuma Idris mutum ne wanda ya yi amanna da ƙudirorin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, musamman wajen abin da ya dace da tattalin arziki da zamantakewar Nijeriya baki ɗaya, ta hanyar Renewed Hope Agenda.

Ya ce: “Idris da ni abokai ne kuma wannan ziyarar ta na alamta burin mu na ciyar da ƙasar nan gaba domin ta zama mai faɗaɗan hanyoyin tattalin arziki kuma mu jawo hankalin duniya zuwa ga sashen ma’adinai a matsayin hanyar jawo wa Nijeriya Jari Kai-tsaye daga Waje, wato ‘Foreign Direct Investment’ (FDI).”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Next Post
Labarin Ƙarya: Babu Inda Gwamna Dauda Lawal Ya Kashe Naira Miliyan 400 Don Tafiye-tafiye

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.