Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi gwanjon rigunan wasa shida daga cikin rigunan da dan wasa Lionel Messi ya saka a lokacin wasannin Argentina a gasar cin kofin Duniya ta 2022 da aka yi a Katar.
Kyaftin Messi, mai shekara 36, ya daga kofin ne bayan da suka doke Faransa a wasan karshe na gasar bayan da aka tashi wasa 3-3 a wata fafatawa mai ban sha’awa da kasashen biyu suka gwabza.
- Samar Da Ci Gaba A Bangaren Ma’adinai: Ministan Yaɗa Labarai Ya Yaba Da Koƙarin Takwaransa Na Ma’adinai
- Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Daliban Borno Gida Bayan Kammala Karatunsu A Kano
Rigarsa ta wasan karshe na kunshe cikin jerin rigunan da ake sa ran za su samu sama da fam miliyan takwas a gwanjon da Sotheby ta shirya a Birnin New York na kasar Amurka.
Rigar kwallon kafa wacce ta fi daraja ita ce ta tsohon dan wasa Diego Maradona da ya sanya a gasar Kofin Duniya ta shekarar 1986, wacce aka sayar kan fam miliyan 7.1 a shekarar 2022.
Brahm Wachter, shugaban masu tara kayayyaki na zamani na Sotheby, ya ce sayar da riguna shida na Messi “ya zama babban abin alfahari a tarihin gwanjon kaya” na duniya da aka taba yi.
Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, ya zama dan wasa na farko a tarihin gasar Kofin Duniya da ya ci kwallo a kowanne mataki a gasar, tun daga rukuni har zuwa wasan karshe.