Kasar Qatar da ke sulhu a tsakanin Isra’ila da Hamas ta bayyana a daren ranar Litinin cewa an tsawaita tsagaita bude wuta tsakanin sojojin Isra’ila da na Hamas a Gaza da kwanaki biyu.
Jami’an Hamas sun ce, tsawaita tsagaita bude wuta a tsakanin bangarori biyun yana nan akan dokoki da sharuda kan yarjejeniyar da aka cimma ta tsagaita bude na kwanaki hudun farko, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
- Kasafin Kuɗin 2024: A Jihar Katsina, Ɓangaren Noma Zai Samu Kashi 6.21% Kawai – Kwamishina.
- Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Soke Zaben Kakakin Majalisar Kaduna
A daren Litinin ne ya kamata a kawo karshen tsagaita wuta na kwanaki hudu na farko.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar ne ya fitar da sanarwar tsawaita tsagaita bude wutar a cikin wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X cewa, an cimma yarjejeniyar tsawaita tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki biyu a zirin Gaza.
Kawo yanzu dai babu wani bayani daga Isra’ila, amma wani jami’in fadar White House (Gidan gwamnatin Amurka) ya tabbatar da cewa an cimma matsaya.