Tsohon shugaban hukumar zabe mai zabe, INEC), Attahiru Jega ya bukaci Shugaban kasa, Bola Tinubu da ya sake duba nadin kwamishinonin zabe, inda ya ce har yanzu lokaci bai kure ba.
Jega ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan tanabijin na Channels kan harkokin siyasa.
- Sama Da Kamfanoni 5,600 Ne Suka Shiga Baje Kolin Sassan Motoci Na Shanghai
- Kamfanonin Siminti Ke Haifar Da Kashi 7 Na Dumamar Yanayi A Duniya – Dangote
Ya ce, “Ina tunanin ko shakka babu idan har shugaban kasa yana saurare, shawarata ita ce ka gaggauta duba nadin kwamishinonin zabe da majalisar dattawa ta amince da su kwanan nan.
“Yana da matukar muhimmanci saboda a bayyana yake cewa nadin ya nuna wani sakon kuskure game da aniyar gwamnati na inganta sahihin zabe, yana kuma nuna cewa akwai halin ko-in-kula game da kare ‘yancin kai da nuna son kai na hukumar gudanar da zabe.
“Na tabbatar da cewa ko dai an yi wa shugaban kasa bayanin ba daidai ba ko kuma ba a ba shi cikakken bayani game da wadannan nade-nade ba. Wannan ita ce shawara ta farko da zan bayar, domin bai yi latti ba.
“An tabbatar da cewa mutanen da aka nada ‘yan wasu bangare ne ko kuma mambobin jam’iyyun siyasa ne hakan ya saba wa kundin tsarin mulki. Ya kamata a yi abin da ya dace, kuma a yi gyara,” in ji shi.
Tsohon shugaban INEC ya ci gaba da cewa, “Na biyu shi ne, majalisar dattiwa da kanta na bukatar ta shi tsaye. Abin da aka saba yi, idan aka ba da irin wadannan shawarwari, shi ne a aika wa kwamitin da ke da lokacin yin nazari mai zurfi kan duk mutanen da aka nada kafin a zo zauren majalisar.
“Amma a wannan lamari, daga duk abin da muka ji kuma muka karanta, ya nuna cewa maganar ba ta je gaban kwamitin ba, kawai ya je zauren majalisar dattawa kai tsaye kuma suka yi gaggawar amincewa da su.
“Don haka, ko da kyakkyawar niyya aka yi, an bi tsarin da ba daidai ba, kuma wannan tsari na kuskure ne ya sa a yanzu ana nada mutanen da ba su dace ba a cikin irin wadannan mukamai.”