Rikicin tsarin mulki ya kunno kai yayin da Majalisar Dattawan Nijeriya ta zartas da wani kuduri na neman Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya hana wa kananan hukumomin da ba su zabi shugabanni ba kudadensu.
Sai dai kudurin majalisar dattawan ya saba wa hukunce-hukuncen kotun koli, inda ta bayyana cewa shugaban kasa ba shi da hurumin hana kudaden da ake ware wa jihohi da kananan hukumomi.
- Za A Shiga Mummunar Damuwa A Gaza Idan Ba Ku Dauki Mataki Ba – Gargadi Ga Majalisar Tsaro Ta MDD
- Badakala: Majalisar Wakilai Ta Bayar Da Umurnin Cafke Gwamnan CBN, Babban Akanta Na Kasa Da Sauransu
Tuni dai kudurin ya fuskanci suka na ganin yadda ‘yan majalisar ke kokarin yin adawa da hukuncin kotun koli.
Akwai jihohi da dama da ba su gudanar da zaben kananan hukumomi ba, inda kantomomin ne ke jan ragamar tafiyar da kananan hukumomin.
A wani taron zaman majalisan, ‘yan majalisar dattawan sun bukaci Shugaba Tinubu ya rike kudaden kananan hukumomin da ba su yi zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli ba.
Hakan ya biyo bayan kudurin da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro ya gabatar wanda ya koka da gazawar wasu gwamnatocin jihohi wajen gudanar da zaben kananan hukumomi.
Bisa gabatar da wannan kuduri ne majalisar dattawan ta bukaci bangaren zartarwa da ta hana wa kananan hukumomin da ba za a zaba ba kudadensu.
Kudurin ya yi Allah wadai da rusa zaben shugabannin kananan hukumomin a Benuwai da sauran jihohin Nijeriya.
Ya bukaci gwamnan Jihar Benuwai da ya kiyaye rantsuwar da ya yi na yin biyayya ga doka da kuma kare kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya.
Kudurin majalisar dattawan ya yi kira da gwamnan ya sake yin nazari a kan rusa zababbun shugabannin kananan hukumomi tare da dawo da su nan take.
Sanata Abba Moro, mai wakiltar Benuwai ta Kudu wanda shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa ya ce ya damu matuka kan rusa zababbun shugabannin kananan hukumomi da kansilolin da aka yi a Jihar Benuwai.
Da yake bayar da gudunmuwarsa a kan muhawarar, Sanata Adams Oshiomhole mai wakiltar Edo ta Arewa ya ce a halin yanzu kusan jihohi 16 a Nijeriya ba su da zababbun shugabannin wadanda aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.
Ya ce ya kamata majalisar dattawa ta umurci ministan kudi ya dakatar da bayar da kudade ga kananan hukumomin da ba su da zababbun shugabannin da kansiloli. Shawarar ta kuma samu goyon bayan babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume.
Har ila yau, Sanata Abdulfatai Buhari da ke wakiltar Oyo ta Arewa ya tabo wani batu na daban, ya ce kamata ya yi a gyara dokar zabe ta yadda za a bai wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) damar gudanar da zaben kananan hukumom