Shafin da ke zakulo muku fasihan marubuta manya da kanana. A yau ma shafin na tafe da fasihiyar marubuciyar littafin Hausa, wato FAUZIYYA USMAN. Inda ta bayyanawa masu karatu yadda ta tsinci kanta a fannin rubutu. Ga dai tattaunawar tare da FATIMA ZAHRA MAZADU Kamar haka:
Ya sunan Malamar?
Sunana Fauziya Usman
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Ni ‘yar Jihar Zamfara ce ina zaune a garin Gusau, a nan na yi dukka karatu na kuma har yanzu ina cikinta.
Me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutu?
To gaskiya ba zan ce ga wani abin da ya ja hankali na ba, kwatsam na samu kaina a cikin rubutun littafi.
Wanne irin labari ki ka fi maida hankali a kai wajen rubutawa?
Gaskiya ni ko ina, ina tabawa to ba wani wanda na fi maida hankali.
Ya farkon fara rubutun ya kasance?
Gaskiya na samu farin ciki sosai saboda ban samu wani kalubale ba.
Ya gwagwarmayar farawar ya kasance?
Gaskiya ba wata gwagwarmaya dana samu a kai.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar musu kina son fara rubutu, shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su?
Abin shi ne ko da na fara rubutu na yi aure, sannan kuma mujina ya karfafamin tare da bani kwarin guiwa sosai.
Daga lokacin da ki ka fara, kawo iyanzu kin rubuta labari sun kai kamar guda nawa?
Gaskiya Alhamdulillah na rubuta littattafai da dama wadanda yawansu zai kai 30.
Wanne littafi ne ya zamo bakandamiyarki cikin littattafan da ki ka rubuta?
Muma ‘Ya’ya ne.
Wanne labari ne ya fi baki wahala lokacin da ki ke rubutawa, kuma me ya sa?
Da’iman muna tare, saboda yana tare da kunci wanda har sai da ya saka ni zubar da kwalla.
Cikin labarin da ki ka rubuta akwai wanda ki ka buga ko ki ke sa ran bugawa?
Ba wanda na buga amma da akwai wadanda nake son na buga in sha Allah.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta game da rubutu ko masu karatu?
Eh! na samu kalubale a littafin Da’iman muna tare da burin iyayenmu shi ne namu.
Wanne irin Nasarori ki ka samu game da rubutu?
To Alhamdu lillah na samu nasarori sosai, musamman tarin masoyan da nake da su, ko yaushe suna yi min fatan alkhairi hakan yana yi min dad’i sosai.
Ya kika dauki rubutu a wajenka?
Hmm rubutu babban al’amari ne wanda yake da matukar girma sosai, kamar dai yanda yake al’kalami ya fi takobi tabbas wannan gaskiya ne
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Ina da burin zama babba kuma shahararriyar marubuciya, wacce mutane da dama za su santa sannan kuma su yi alfahari da ita.
Ko akwai wadda ta taba bata miki rai game da rubutunki ko aka yaba?
Eh duka a na samu.
Wanne abu ki ke tunawa ki ke jin dadi game da rubutunki?
Masoyan da nake da su musamman masu yi min fatan alkhairi.
Bayan rubutu kina wata sana’ar ne?
Eh ina yin sana’a da dama.
Ya ki ke iya hada sana’arki da rubutu?
Ko wannen su yana da lokacin dana bashi.
Kamar wanne lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Gaskiya nafi jin dadin rubutu da dare.
Me za ki ce da makaranta labaranki?
Tsakanina da su sai godiya da kuma fatan alkhairi.
Gaida mutum biyar.
Ina gaida masoyiya ta Fatima Mazadu, Maryam Usman (Maman Amira), Firdausi Usman (Ummu Sadik), Zainab ‘yar gata, Umar Dalha.