Kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi a Jihar Taraba, biyo bayan yadda ayyukan ‘yan bindiga ya yi kamari a jihar, wanda hakan ya hana manoma girbe amfanin gonakinsu da suka noma a bana.
Bincike ya nuna cewa, ‘yan bindigar sun hana manoma shiga cikin gonakinsu, don girbe abin da suka shuka a Kananan Hukumomin Bali, Ussa, Takum da kuma Ardo Kola da ke jihar.
Don haka, yanzu farashin buhun masara mai nauyin kilo 100, ana sayar da shi kan naira 32,000, sabanin yadda ake sayar da shi a shekarar da ta wuce kan naira 18,000.
Bugu da kari, farashin buhun shinkafar gida, ana sayar da mai nauyin kilo 100 kan naira 25,000, sabanin yadda ake sayarwa a shekarar da ta gabata kan naira 17,000.
Har ila yau, ‘yan bindigar sun hallaka manoma da dama tare da yin garkuwa da manoma da yawa a fadin wadannan kananan hukumomi.
Wata manomiya mai suna Lami John ta bayyana cewa, ‘yan bindigar sun hana su girbe amfanin gonakinsu a yankin Kwando na Karamar Hukumar Ardo Kola.
Sannan ta sanar da cewa, ‘yan bindigar sun yi sace manoma da dama; ciki har da ita kanta da kuma ‘ya’yanta, amma wasu suka samu nasarar har da ita da kuma ‘ya’yan nata daga dajin da aka kai su.
Bugu da kari, a Kananan Hukumomin Ussa da Takum, an kashe manoma da dama a wasu hare-haren da ‘yan bindigar suka kai a kwanakin baya tare da hallaka manoma da dama, wanda hakan ya jawo manoman suka gaza girbe amafnin da suka noma a gonakin nasu.
Wani manomi mai suna Mista Bulus Andeyake ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kutsa a cikin yankunan nasu, inda hakan ya sa manoma a yankunan su gaza girbe amfanin gonar da suka noma.
Ya ci gaba da cewa, suna sayar da rayukansu ne idan za su tafi gona, domin a ko’ina akwai ‘yan bindigar da ke firgita manoman.
Bulus ya kara da cewa, ‘yan bindigar a ‘yan watannin baya sun sake hallaka wasu manoma goma sha daya a yankin Jenuwagida a lokacin da suke kan girbe amfanin gonarsu.
Kazalika ya sanar da cewa, ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu manoma biyu a yankin Jenuwagida a cikin gonakinsu a makon da ya wuce.
Andeyake ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara kokari wajen yakar wadannan ‘yan bindiga, domin gonakan manoman a yankunan su kubuta.
Shi ma wani takwaransa mai suna Dauda Maihula ya bayyana cewa, manoma da dama na jin tsoron zuwa gonakinsu, domin girbe amfanin gona, sakamakon yadda ‘yan bindigar suka mamaye gonakin nasu.
A cewar tasa, ‘yan bindigar sun kuma kashe mafarauta da dama a wata fafatawa da suka yi da su a makon da ya gabata.
Bugu da kari, wani mai sana’ar sayar da hatsi a kasuwar sayar da hatsi ta Iware, Alhaji Haruna Jafar ya bayyana cewa, farashin kayan abincin zai ci gaba da tashi sakamakon wannan aiki na ‘yan bindiga a wadannan yankuna.
Ya ci gaba da cewa, a yankin Kwando da ke Karamar Hukumar Ardo Kola da kuma yankin Dakka a Karamar Hukumar Bali, ‘yan bindigar sun karbe yankuna da dama wanda manoman ke zaune.
Haka zalika ya sanar da cewa, hakan ya jawo hana manoman yankunan girbe amfanin gonakinsu da suka noma.
Ya kara da cewa, manoma da dama da suka noma shinkafa, masara, waken soya da farin wake, sun gaza girbe amfanin sakamakon wadannan hare-hare na ‘yan bindiga.
Kazalika, a karshe ya kuma yaba wa mafarauta da sauran jami’an tsaro, kan kokarin da suke yi na yakar wadannan ‘yan bindiga a yankunan.