Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa Ta Nijeriya (NCDC), ta ba da rahoton bullar cutar Korona guda 880 a ranar Asabar, wanda ya kai 258,517 tun bayan bullar cutar.
Adadin shi ne mafi girman adadin da aka samu na mako-mako tun tsakanin 17 ga Janairu zuwa 23, lokacin da adadin ya kai 1,258.
- Chelsea Ta Sayi Sterling Daga Manchester City
- Sallah: Gwamnan Gombe Ya Bukaci Al’umma Su Rungumi Son Juna, Sadaukarwa, Hadin Kai, Addu’a Ga Kasa
Jihohi bakwai da babban birnin tarayya ne ke gaba wajen yawan masu dauke da cutar daga 2 zuwa 8 ga Yuli.
Jihar Legas, na yawan masu dauke da cutar 750, sai kuma babban birnin tarayya Abuja da aka samu 48, sai kuma Ribas da aka samu mutane 40.
Sauran sun hada da Delta mai mutane 21, Akwa Ibom mai mutane 11, Kano mai mutane biyar, Nasarawa hudu sai Filato mai mutum daya.
Cibiyar ta ce jihohin Abia, Kaduna da Sokoto sun ba da rahoton bullar cutar.
Ya zuwa yanzu, Legas ce ke da mafi yawan adadin masu cutar Korona 101,391, sai Abuja (28,811) sai Ribas (16,866).
Tun bayan barkewar cutar a shekarar 2020, jimillar marasa lafiya 250,388 sun warke daga cutar, inda mutane 3,144 suka rasa rayukansu sakamakon cutar.
A halin da ake ciki, NCDC ta shawarci ‘yan Nijeriya da su yi taka tsantsan yayin bikin babbar sallah sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar a duniya.
NCDC ta ce adadin masu kamuwa da cutar a mako-mako ya karu a duniya a mako uku a jere.