Tun bayan kama aiki gadan-gadan, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya sha alwashin tsaftace Abuja; ciki har da daukan matakan dawo da ainihin tsarin birnin na asali korar ‘yan jari bola a Abuja.
Wannann ya sa LEADERSHIP Hausa ta tattauna da wasu masu sana’ar jari bola domin jin yadda sana’ar take a halin yanzu inda suka nunar da cewa, a halin yanzu kusan komai ya tsaya cik!
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
- Wani Mutum Ya Halaka Sakataren Kotu Har Lahira A Jihar Adamawa
Babban Sakataren Kungiyar ‘Yan Jari Bola da ke yankin Mabushi, Aminu Muhammad Ahmad, wanda ake yi wa lakabi da Malam Bala da kuma Shugaban Kungiyar Masu Sana’ar Jari Bolar ta yankin Suleja, Alkasim Ibrahim, wanda aka fi sani da Alhaji Bage sun nuna takaicinsu a kan yadda aka kasa ganin alherin da sana’ar ke yi wajen tsaftace Abuja.
Aminu Muhammad ya fara da tsokaci a kan gudunmawar sana’ar ga tsaftace Birnin Tarayya Abuja.
“Eh, ka san a kullum matsalar da dan bola yake fuskanta game da gwamnati shi ne, rashin ainihin tabbataccen muhallinsa. Wannan ita ce babbar matsalarmu a cikin wannan sana’a ta jari bola. Amma idan ba don haka ba, a koda-yaushe muna maraba da duk wanda ya ce yana son tsaftace Abuja. Dalili kuwa, mu ne muke bayar da gudunmawar tsaftace garin Abuja da kashi 60 zuwa 70.
Domin kuwa, yadda muke kwashe shara tare da tsaftace Abujan ko Hukumar Tsaftace Muhalli ta Babbar Birnin Tarayya, ba ta yi. Illa dai kawai ita kawai hukuma ce; wadda gwamnati ta kafa domin amfanin wannan bangare, amma dai batun tsaftace Abuja ta kasance babu wani datti, magana ta gaskiya mu masu sana’ar jari bola mu ne muke bayar da kaso mafi tsoka cikin wannan harka.
Game da zargin da ake musu na sace-sacen kayan mutane kuwa, Amina ya ce, “Shi zargi ba a kan dan bola kawai ya tsaya ba. Babu wani bangare wanda ba za ka samu mai kyau da mara kyau ba, matukar jama’a za su hadu ko da mutum biyar ne, sai ka samu wanda a cikinsu ya fi kowa nutsuwa da kuma wanda ya fi gurbacewa. Ba za mu ce ba a zargin mu ba, amma wanda bai san mu ba; shi ne ya ke yi mana irin wannan zargi.
Duk mutumin da ya zauna da mu; ba zai taba zargin mu ba, saboda muna yin iya bakin kokarinmu. Sannan, akwai wadanda a gidajen iyayensu ma; idan aka fada musu ba sa ji, amma idan suka zo cikinmu suka zauna yadda muke kula da su, wallahi ko a gidajen iyayen nasu ba a yi musu abin da muke yi musu. Ba don komai ya sa muke yi musu haka ba, sai don su zama mutane nagari, to amma dai ka san mutum tara yake bai cika goma ba. Wannan ita ce gaskiyar magana, amma ko shakka babu muna yin iya bakin kokarinmu na ganin mun dakile wadanda suke ba nagari ba a cikin namu.”
Aminu ya kuma koka da cewa, a halin yanzu, “wannan sana’a ta shiga halin ha’ula’i, saboda galibin ayyuka sun shafi gidajen bola. Don haka, a nan ba ma mu ne muka shiga halin ha’ula’i ba, illa wasu daga cikin Kamfanonin Nijeriya. Alal misali, ni na fi kowa iya harkar sarrafa leda, kamfanin da nake bai wa wadannan kayayyaki; a cikin kashi daya na kayayyakin da nake ba su yanzu bai fi kashi 50 zuwa 60 suke samu ba.
“Ka ga yanzu wannan abu ai ba karamin nakasu ne, ba kawai ga dan bola ba har ma da kamfanin da kuma kasa baki-daya, tun da mu ne muke ba su wadannan kayayyaki ake sake sarrafawa daga abu mara kyau zuwa mai kyau. Ka ga kuwa ai an samu koma baya, saboda kamfanonin nan da muke bai wa kayayyakin; suna biyan haraji ga gwamnati sannan kuma suna dibar ma’aikata, haka nan wadanda ba su shafi sana’ar ba ma suna cin abinci da ita.
“Har ila yau, ba mu kadai ne muka samu nakasu dari bisa dari ba, akwai mata da yara da manyan mutane wadanda su ma abin ya shafa, domin kuwa dan bola ba ya iya samar da abin da yake samarwa yanzu kamar a da.”
Bugu da kari, sakataren ya bayyana yadda lamarin ke shafar rayuwar iyalansu.
“Bara yanzu na ba ka misali da kaina. Yanzu haka ina da yara hudu, kuma guda biyu suna jami’a, kuma wallahi da wannan sana’a na auri uwarsu, sannan da ita nake ciyar da su in shayar da su. Ka ga kuwa sana’ar bola a wurinmu, babu abin da ba ta yi mana ba.
“Yanzu haka, yarona na farko yana Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Garin Gusau, yayin da macen kuma take Jami’ar Arewa Maso Yamma, sannan kuma dukkanninsu suna aji na biyu. Ka ga kuwa alhamdu lillahi, kazalika muna nan da yawa a cikinmu wadanda ‘ya’yansu ma har sun yi digiri na biyu, duk kuma da wannan sana’a muke tafiyar da al’amuransu na yau da kullum.” In ji shi.
Da yake yankin Suleja na makotaka da Abuja, LEADERSHIP Hausa ta tattauna da Shugaban Kungiyar Masu Sana’ar Jari Bola ta Suleja, Alkasim Ibrahim domin jin yadda matakan da aka dauka nah ana sana’ar a Abuja ta shafe su.
Ya ce babu shakka lamarin ya shafe su kai tsaye, domin a cewarsa mafi akasarin kayan da suke samu su saya su sarrafa daga cikin Abuja ake kawo musu, sannan wadansunsu ma duk yaransu ne a can Abujar.
“Duk yawancin yaran, an fatattake su ba ma sa yin sana’ar kwata-kwata, baya ga kalubale da muke fusakanta. Haka zalika, kamar dai ita wannan sana’a tamu mu ‘yan kasa mu ne muka fi yin ta, musamman ma mu al’ummar Hausawa, amma yanzu kamar China suna nema su kwace harkar ya zamanto sana’ar ba ma yin ta, tun da su ne suke bin wuraren da muke zuwa mu sayo, kamar wadanda suke zuwa su tsinto mu kuma mu je mu tattara mu sayo mu kawo nan mu sarrafa shi, to su ma yanzu suna bi can wuraren, maimakon ma su zo wurinmu a’a sai su je can wurin su rika saya, in abu naira 100 ne su kuma sai su saya 150, to a yanzu dai shi ne babban kalubalen da ke gabanmu,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “wannan doka da aka kafa a Abuja ta shafe mu, amma dai babban kalubalenmu shi ne, wannan shigowar ta ‘yan China, don haka ne muke son gwamnati ta shigo ciki ta tabbatar da wannan sana’a tamu, in dai mu ‘yan kasa ne za mu yi to a bar mana mu yi, idan kuma suna so za su yi to su biyo ta hannunmu, wannan shi ne dokar da muke so gwamnati ta aiwatar mana.”
Da aka tambaye shi ko sun shigar da koken nasu ga gwamnati, duba da yadda gwamnatin ke sauraron koken kungiyoyi? Ya ce, “a gaskiya wannan koke mun sha shigar da shi, kai har wadansu kudade muka biya muka je Abuja da nufin za a ba mu tallafi, amma a karshe har yanzu dai ba mu ga wani abu da ya canja ba. Duk kuwa da cewa, muna bukatar lallai gwamnati ta shigo ta tallafa mana da jari, domin ci gaba da kula da wannan sana’a tamu, don kuwa muna samar wa da dimbin matasa aikin yi maza da mata karkashin wannan sana’a.
“Ba maza ba har mata abin ya shafa, domin mata ne suke gyara mana kayanmu, a duk yayin da muka dauko wadannan kaya, su ne suke barewa su kwance murfayen; idan ba ka sani ba, sama da mata dari biyu ne suke yi mana aiki a baya; amma yanzu aikin sai ya kasance idan an yi sati kafin wani satin ya zagayo babu wani aikin, saboda karancin kayayyakin. A da wurin da muke samo kayan da zarar mun je muke samun su a jiye, amma yanzu wadannan bakin ‘yan China da suka zo, su ne suke zuwa su kwashe mu ba ma karuwa da komai, mun zama ‘yan kallo.
“Wani kalubalen da muke sake fuskanta a halin yanzu shi ne na tsadar kayayyaki, abin da muke saya naira 30 yanzu ya zama 200, to ka ga a da idan kana da naira 300,000, za ka samo adadin wanda za ka dauko ko da Tirela guda ne, amma yanzu sai ka sa naira miliyan 1, 500,000 sannan ga shi yanzu babu wannan kudi, domin yanzu idan ka sa karamin jari kamar miliyan daya da rabi, idan ba ka yi da gaske ba sai ka neme ta ka rasa, tun da wani kayan idan ka sayo ba za ka maida kudinka ba, idan kudin dako a da naira 10,000 ne, yanzu sai ka biya 40,000, sannan kuma mu kayan bai kara wata daraja a wurinmu ba.” In ji shi.
Martanin Hukumar Kare Muhallin Abuja
Da aka tuntube ta kan matakan da suka dauka na fatattakar masu wannan sana’a maimakon gyara ta zuwa turbar da ta dace, mai mai magana da yawun Hukumar Tsaftace Babban Birnin Tarayya Abuja (AEPB), Janet Peni ta bayyana cewa, suna daukara ‘yan jari bola ne a matsayin barazana ga harkokin tsaro, sakamakon mafi yawancinsu masu aikata laifi ne.
Ta kara da cewa, “akwai wani bangare na hukumar da ke kula da Abuja da ke cafke ‘yan jari bolar a duk inda suka gan su, domin mafi yawancinsu masu aikata laifuka ne iri daban-daban.”