Ministan Ma’adanai, Dele Alake, da takwararsa na Tsaro, Abubakar Badaru, sun kammala tattauanwa a kan yadda za su fitar da tsari namusamman don tabbatar da tsaro a filayen hakar ma’adana a fadin tarayyar Nijeriya.
Da yake jawabi bayan ganawar sirri da suka yi, Ministan Tsaro, Badaru ya ce, shirin samar da tsaron na daga cikin tsare-tsaren shugaban kasa Bola Tinubu ya fito da su na kawar da ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma ayyuykan ‘yan ta’adda a sassan Nijeriya.
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
- Saurayi Ya Kashe Budurwarsa A Kan 5000 A Bauchi
“Nijeriya na son tatsar kudin shiga mai yawa daga bangaren ma’adanai amma lamarin rashin tsaro ya addabin bangaren, a kan haka ministan yake kokarin ganin an samar da cikakken tsaro a yankunan da ake hakar ma’adanai,” in ji Badaru.
“A kan haka muka tattauna a kan hanyoyin da za mu kare yankuna da ake hakar ma’adanai tare da samar da cikakken zaman lafiya ta yadda harkar hakar ma’adanai zai buunkasa, Nijeriya ta ci gaba da samnun kudaden shiugar da ya kamata.”
Ya kuma bayyana cewa, kwai shiri na musamman da gwamnati take yi na samar da wata runduna da za a kira da ‘Mining Police’ da za su yi aikin tabbatar da tsaro a wuraren da aka fi tayar da hankali a cikin wuraren da ake hakar ma’adanai a kasar nan.
A nasa jawabin, Alake, ya yi gargadi ga masu hakkar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da su kuka da kansu in suka shiga hannun hukuma, ya kuma yi alkawarin goyon baya ga masu gudanar da harkokin su cikin bin doka da oda.