Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da rufe ofishin jakadancinta da ke Yamai a hukumance, matakin da ta ce ta dauka ne har sai abin da hali ya yi.
Sanarwar ta ranar Talata, ta kara bayyana yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin Jamhuriyar Nijar da tsohuwar uwar gijiyarta Faransa.
- Zargin Sata: Jami’an ‘Yansanda A Kaduna Sun Kama Buhunan Taki Guda 600
- AFCON 24: Yusuf Alhassan Ya Maye Gurbin Ndidi A Cikin Tawagar Yan Wasan Nijeriya
Lamarin dai ya samo asali tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa tsohon shugaba Bazoum Mohamed a watan Yulin 2023.
Cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen Faransa, ta ce an shafe watanni akalla biyar ana dakile duk wasu ayyukan ofishin jakadancin kasar da ke Nijar, matsalolin da suka hada da hana ma’aikatansu tafiye-tafiye, da kuma hana kai musu ziyara.
A cewar Faransa matakan sun sabawa yarjejeniyar diflomasiyyar kasashen suka rattaba wa hannu a birnin Vienna, cikin shekarar 1961.
A karshen watan Disamban 2023, Faransa ta fara daukar matakin dakatar da ayyukan ofishin jakadancin nata na Nijar, da bayan dimbin ma’aikatan diflomasiyarta suka fice daga kasar sakamakon tsangwama da neman afka musu da wasu fusatattun mutane suka rika yi.