Katsina babban gari ne mai tarihi a Arewacin Nijeriya kamar yadda aka samu Katsina na daga cikin Hausa bakwai na gaskiya. Katsina ta fara bunkasa ne a karni na 10 zuwa na 11. Addinin musulunci an fara shi a 1450 Muhammadu Korau shine Sarkinta na farko Muhammad Korau wanda ya yi sarauta a kusan karshen karni na 15. Lokacin mulkinsa ayarin fatake kan Rakuma suna suna tafowa ta Sahra daga Ghudāmis (Ghadames),Tripoli, da kuma Tunis a kudanci zuwa Katsina suna kawo abubuwan alheri zuwa garin, ta haka ne aka fara samun takun saka na zaman Doya da Mai tsakanin manyan daulolin Afirka ta yamma na Songhai da Songhai (Gao) da Bornu.A karni na 1513 Songhai ta ci Katsina da yaki.
Ganuwar Katsina ta ainihi an gina su ne a tsakanin karni na-16.A shekara ta 1554 Katsina ta samu galaba kan dakarun Songhai sai 1570 ta gma da na Kano da ta kasance babbar abokiyar adawarta ta al’amarin da ya shafi fatauci. Bayan da dakarun Maroko sun gama da Songhai a 1591, Katsina a wancan lokacin tana DA alaka da Bornu.Katsina ta shiga yanayin ci gaba a farkon karni na 18. Wannan ya hada da kasancewarta babbar cibiya ta kasuwanci a kasar Hausa ta maye bayan Timbuktu (Tombouctou) a matsayin cibiya ta al’amuran da suka shafi nazarin musulunci a Afirka ta yamma.Duk a wancin karni akwai yakin da tayi da Gobir a Arewa maso yamma wanda shi ne ya kasance mafarin komawar bbayan Katsina.
- Mahara Sun Halaka Wasu ‘Yan Kasuwa 8 A Katsina
- ‘Yadda Aka Yi Garkuwa Da Ni, Bayan Musanya Min Jariri A Asibiti’
Fulani sun iso Katsina ne a karni na 15 a shekarar 1804 sai ga jihadin Usman Dan Fodio,wanda aka samu ‘yar tangarda da farko an fara ne da Gobir. Shugaban Fulani Umaru Dallaji shi ya mamaye birnin Katsina a shekarar 1806 ya zama Sarkin bayan jihadin Danfodiyo shine Sarki na farko.A lokacin masarautar tana ansar umarni ne daga wakilin Sultan na Sakkwato wani gari mai nisan mil 160 ko kilomita [258).Manyan mutane sun bar Katsina inda suka koma Dankama mai mil 25 ko [ kilomita 40] a Arewa ta gabas) zuwa Tassawa (Tessaoua) da Maradi Maradi a Niger,inda suka samar da Hausa ta Masarautar Katsina.Harin da aka kai na karni na gaba dayan karni na 19 ya nakasa Sarkin Fulani da garin Katsina wanda a lokacin Kano ta sha gabanta.
A shekarar 1903 Sarkin Katsina ya ba da kai ga Turawan mulkin mallaka na Ingila da suke Arewacin Nijeriya. Lokacin da Turawan Ingila da Faransa suka fidda iyakar Nijeriya da Nijar a shekarar 1904, an rage masarautar inda aka maida wani wuri zuwa Kano Kano. Sai dai kuma yawancinwuraren yanzu suna karkashin Jihar Katsina.