A kokarin da yake yi na inganta harkar ilmi da ababen more rayuwa a mazabarsa, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Demsa/Numan/Lamurde a majalisar tarayya ya kaddamar da rukunin ajujuwa 3 a unguwar Kodomti da ke karamar hukumar Numan.
Da yake jawabi a ranar Laraba a wajen taron, dan majalisar ya koka kan matsalar karancin ababen more rayuwa a mafi yawan al’ummar mazabar, inda ya jaddada kudirinsa na ganin an inganta ilimi a lokacin mulkinsa.
- Kotu Ta Raba Auren Shekaru 7 Saboda Rashin Soyayya
- Wata Mata Ta Sace Jariri Sabuwar Haihuwa A Asibiti A Nasarawa
Dan majalisar ya bayyana cewa ingantaccen yanayin koyon karatu yana da muhimmanci ga rayuwar yara, don gudanar da ingantaccen koyo.
Bayan bayar da tallafin karatu ga dalibai a matakai daban-daban na ilimi, ya jaddada cewa tare da ilimi ya zo da ‘yanci, tare da yin alkawarin kara tsoma baki a fannin.
Dan majalisar ya yi amfani da wannan damar wajen nuna godiya ga irin goyon bayan da ya samu daga jama’ar mazabarsa tare da yin alkawarin ba zai taba bata ba su kunya ba.
Al’ummar mazabar Kodomti karkashin jagorancin su Ndewodi Kodomti da Ha Shaforon, sun cika da farin cikin bisa kaddamar da ginin ajujuwa.
Jama’a da dama sun fito don nuna godiya ga dan majalisar, sun yi addu’ar Allah ya taimaki dan majalisar ya samu nasara a duk kokarin da yake aikin inganta rayuwar al’ummar mazabarsa.
Al’ummar Kodomti ta yi fice wajen noma da kamun kifi, sun gabatar da kyautar kifi katann guda ga dan majalisar, a matsayin alamar kauna da godiya.
Abubuwan da suka fi daukar hankali a taron sun hada da gabatar da al’adu da al’ummar Kodomti da Bandawa suka nuna.
A nasu bangaren, daliban makarantar firamare ta Kodomti sun gabatar da jawabai da dama cikin wakoki da kasidu domin nuna godiya ga dan majalisar tarayyar.
Cikin manyan bakin da suka halarci bikin sun hada da Ndewodi Kodomti, Ha Shaforon, Hon. Pwamwakaino Makondo, shugabannin kananan hukumomin Numan da Lamurde.
Shugabannin jam’iyyarsa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a Numan, Demsa Lamurde duk sun halarci taro.
Haka kuma dan majalisa Kwamoti B La’ori, ya ziyarci kasuwar Numan, domin jajanta wa ‘yan kasuwar da iftila’in gobara ya kone musu shaguna kurmus.
Ya yi fatan Allah ya tsayar da lamarin haka, sannan ya yi alkawarin tallafa musu.