Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara shirin ilimantar da matasa a matsayin daya daga cikin hanyoyin magance matsalar tsaro da ta addabi wasu yankunan kasar nan.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da littafin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
- Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Wajen Taron Dandalin Tattauna Tattalin Arzikin Duniya
- Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi: NNPP Ta Baiwa Al’ummar Kano Tabbacin Gudanar Da Sahihin Zabe
Sai dai har yanzu ana ci gaba da kai munanan hare-hare musamman a Arewacin Nijeriya duk da alkawarin da shugaban ya yi a lokacin yakin neman zabensa.
Yanzu haka babban birnin tarayya, Abuja na fuskantar karuwar sace-sacen mutane a manyan tituna da kuma gidaje a baya-bayan nan.
Tinubu ya yi Allah-wadai da sace-sacen da aka yi na baya-bayan nan sannan ya kudiri aniyar kawo karshen lamarin.
“Babu wani makami da zai yaki talauci da ya kai karfin ilimi,” in ji shi.
“Hukumomin tsaro suna aiki tare da tura dakaru don magance kalubalen da ake fuskanta nan da nan, yayin da kuma za a samar da dukkan abubuwan da ake bukata, da manufofi da tsare-tsare nan ba da jimawa ba don ilimantar da matasan Nijeriya.”
Yanzu haka dai, mazauna wajen Abuja, sun fara yin hijira a daidai lokacin da ake samun yawaitar sace-sacen mutane don neman kudin fansa.