Babbar darektar hukumar cinikayya ta duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata tattaunawarsu a ranar Alhamis da ta gabata a gefen taron dandalin tattalin arzikin duniya da aka gudanar a Davos cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.
Tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO fiye da shekaru 20 da suka gabata, kasar Sin ta zama kasa mafi girma a fannin cinikayyar kayayyaki a duniya, kuma babbar abokiyar huldar kasuwanci ga kasashe da yankuna sama da 140, wadda take ba da gudummawar kusan kashi 30 cikin dari ga ci gaban tattalin arzikin duniya na shekara-shekara.
- Wang Yi Ya Yaba Da Dankon Zumunci Tsakanin Sin Da Kasashen AfirkaÂ
- Xi Jinping Ya Bada Muhimmin Umarni A Wajen Bikin Bayar Da Lambar Yabo Ta Injiniya Ta Kasa
Okonjo-Iweala, yayin da take bayyana muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa wajen habaka cinikayyar duniya da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya, ta ce, “Duk abin da ya faru da kasar Sin yana yin tasiri ga duniya, hakan ya sanya taka rawar ganin tattalin arzikin kasar Sin ya kasance maslahar kowa da kowa.”
A cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin, GDP na kasar Sin ya samu karuwar kashi 5.2 cikin 100 a shekarar 2023 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2022, wanda ke nuna gagarumar farfadowa bayan COVID-19.
“Kasar Sin tana taka rawar gani sosai, kuma muna son ganin tattalin arzikin kasar Sin ya farfado da karfi, domin hakan zai sa kaimi ga bunkasuwar cinikayya a duniya, da ma bunkasuwar duniyar baki daya, ba wai Sin kadai ba, har ma da sauran kasashen duniya” a cewar ta.
Da take yabawa rawar da kasar Sin ta taka wajen kare tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, Okonjo-Iweala ta ce, “a mahangar kungiyar WTO, Sin ta kasance mai goyon bayan tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, da ra’ayin cudanyar bangarori daban-daban.” (Yahaya)