Jami’an tsaro sun ceto wasu ’yan mata biyar ‘yan uwan Marigayiya Nabeeha da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a unguwar Bwari da ke Abuja.
LEADERSHIP ta rawaito cewa an yi garkuwa da wasu ‘yan uwan juna ‘yan gida daya su shida a Unguwar Bwari da ke Abuja a ranar 2 ga watan Janairu 2024.
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Dan Shekara 7 Bayan Garkuwa Da Mutum 10 A Abuja
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Abuja, Sun Yi Garkuwa Da Mutane 9
Masu garkuwa da mutane sun kashe daya daga cikin mai suna Nabeeha a makon jiya. Bayan kashe wani dalibi da ke karatun digiri, an ce barayin sun bukaci fansar kudi daga Naira miliyan 60 zuwa Naira miliyan 100, yayin da suna masu barazanar kashe sauran ‘yan uwa matan da ke hannunsu.
A ranar Lahadin da ta gabata ne tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Nijeriya, Farfesa Isa Pantami, ya sanar da bukatar neman tara Naira miliyan 50 ga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su don jama’a su taimaka a biya kudin fansar ‘yan matan don ganin an sako sauran ‘yan matan. .
Daya daga cikin ‘yan uwan Najeeba da suka kubuta, ta bayyana irin halin da suka shiga a cikin sakonta da ta wallafa a shafin X (Twitter) don nuna godiya ga ‘yan Nijeriya biyo bayan ceto su da jami’an tsaro suka yi.
“Ina matukar godiya da addu’o’inku da goyon bayanku a tsawon wannan lokacin jarabawar. Wannan shi ne mafi girman jarabawar a rayuwata wallahi amma da yake rahmar Allah na da fadi, ga shi komai ya zo karshe, Na gode muku gabadaya.” Cewarta.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce ‘yan uwa mata tare da wasu da aka yi garkuwa da su a yankin Bwari, jami’an tsaron sun ceto su ne daga dajin Kajuru na jihar Kaduna.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa an ceto ‘yan uwa ‘yan matan da wasu da aka yi garkuwa da su a wani dajin da ke makwabtaka da jihar Kaduna tare da hadin guiwar jami’an tsaro.
“Jami’an sun yi nasarar ceto wadanda abin ya shafa a dajin Kajuru a jihar Kaduna da misalin karfe 11:30 na daren ranar Asabar 20 ga watan Janairu, 2024,” cewar Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, Josephine Adeh.