Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen sake gudanar da zabukan da za a gudanar a mazabun majalisun jihohi hudu na jihar Bauchi.
Kwamishinan zabe na jihar, Mohammed Nura, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN), ranar Lahadi a Bauchi.
- Zaben Cike Gurbi: Masu Kada Kuri’a Miliyan 4.5 Za Su Yi Zabe A Fabrairu – INEC
- Gidan Da Aka Farmaka A Bauchi Ba Na Shugaban INEC Ba Ne – Oyekanmi
“Hukumar za ta sake gudanar da zabukan cike gurbi na zaben 2023, kamar yadda kotun sauraren kararrakin zabe ta bayar da umarni.
“Akalla mazabu 42 ne umarnin kotu ya shafa wadanda za a gudanar da zabukan cike gurbi a jihar Bauchi.
“An shirya gudanar da zabukan a lokaci guda a dukkan mazabun da abin ya shafa a ranar 3 ga watan Fabrairu,” in ji shi.
Nura ya lissafa mazabun da suka hada da Bauchi ta tsakiya; Zungur/Galambi, Madara/Chinade and Ningi 1.
Ya ce za a gudanar da zabe a rumfunan zabe 10 da ke Bauchi ta tsakiya, da rumfunan zabe 12 a Zungur/Galambi, da rumfunan zabe 10 a Madara/Chinade da kuma rumfunan zabe 10 a Ningi ta tsakiya.
A cewar Nura, hukumar za ta fara daukar ma’aikatan wucin gadi tare da gudanar da taron kwamitin tuntuba kan harkokin tsaro (ICCES) a mako mai zuwa.
Ya bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su baiwa hukumar hadin kai tare da bin dokokin zabe domin gudanar da aikin ba tare da wata matsala ba.