Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta ce bata kama shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo ba, sabanin rahotannin da ake yadawa.
Da yake amsa tambayoyi, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya ce “Bello Bodejo ba ya tare da DSS.”
- AFCON 2023: An Samu Daukewar Wutar Lantarki A Wasu Yankunan Kasar Cote d’Voire Sakamakon Shan Kashi
- Sin Ta Ba Da Rahoton Fadada Shigo Da Kayayyakin Gona Da Na Abinci A Shekarar 2023
An kama Bodejo ne a ranar Talata a babban ofishin Miyetti Allah a Tundun Maliya a Babban Titin Abuja zuwa Keffi a Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa.
Mutane da dama sun yi tsokaci a shafukan sada zumunta, cewa ana kyautata zaton jami’an DSS ne, suka kama shugaban da yammacin ranar Talata.
An kama Bodejo ne saboda fargabar kan kirkiro kungiyar ‘yan banga ta Nomad wadda ka iya haifar da tashin hankali a nan gaba.
Ana zargin kungiyar ba ta da rajista da jami’an tsaro, wanda yake wani sharadi da ake bukata kafin kafa wani abu da ya shafi tsaro a Nijeriya.
Idan dai za a iya tunawa, bayan kafa kungiyar ‘yan banga, Bodejo ya jaddada cewa ‘yan bangar za su bi dokokin kasar nan a lokacin gudanar da ayyukansu.
Bodejo, yayin da yake jawabi yayin kaddamar da ‘yan bangar a garin Lafia na jihar Nasarawa, ya bukaci ‘yan sa-kan da su hada kai da ‘yansanda, sojoji, da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a fadin kananan hukumomi 13 na jihar.