Tawagar jami’an tsaro da suka kunshi ‘yansandan kwantar da tarzoma, ‘yansanda da kuma ‘yan banga ne suka yi dirar mikiya gidan fitacccen malamin addinin islama, Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da nufin kama shi.
Makusantan malamin sun shaida ma wakilinmu cewa jami’an tsaron sun je gidan malamin ne da karfe biyar na asuba ranar Alhamis a kokarinsu na ganin sun cafke malamin, sai dai ba su samu nasarar kamun ba zuwa hada wannan rahoton.
- FIRS Ta Tattara Harajin Tiriliyan N12.374 Fiye Da Wanda Ta Yi Alkawarin Tarawa A 2023
- Ba Za Mu Aminta Da Ɗauke Babban Bankin Nijeriya Zuwa Legas Ba – Kungiyar Matasan Arewa
Wasu majiyoyi sun ce jami’an tsaron da suka je gidan malamin za su haura mutum 200.
Idan za a tuna dai babban kotun Shari’a ta daya da ke Bauchi tuni ta bai wa jami’an tsaro umarnin kamo malamin gami da gurfanar da shi a gabanta bisa kin amsa gayyatar da kotun ta masa.
Sai dai tuni malamin ya ce ba zai je kotun ba bisa dalilinsa na cewa ya daukaka kara kan tuhumarsa da ake yi da laifin tada zauye tsaye da kalaman tunzura jama’a da ka iya barazana ga zaman lafiya.