A yayin da aka kammala zabukan kasa na shekarar 2023 da kuma shari’un zabe da aka yi ta tafkawa har zuwa kotun koli, a halin yanzu kallo ya koma bangaren muliki da yi wa al’umma aiki don bunkasa rayuwarsu.
Amma kuma tsarin dimokuradiyya mai inganci ba wai bangaren masu tafi da mulki kawai yake ba muhimmanci ba, har ma da bangaren masu adawa, don su ne ke sa ido don tabbatar da masu gudanar da mulki suna aiki yadda ya kamata, tare da kuma sa ido a kan yadda ake kashe kudaden al’umma.
- AFCON 2023: An Fitar Da Jadawalin Zagaye Na 16
- FIRS Ta Tattara Harajin Tiriliyan N12.374 Fiye Da Wanda Ta Yi Alkawarin Tarawa A 2023
Babu tantama, muryar ‘yan adawa na da muhimmanci a harkar dimokuradiyya, kamar yadda muka gani a Nijeriya tun da aka dawo da mulkin dimokradiyya a wannan zangon a shekarar 1999.
Wannan bangaren na masu adawa zai zama wani dandamali na samar da wasu shawarwari da tsare- tsaren yadda za a tafi da harkokin gwamnati koma bayan wanda gwamnati mai ci ke aiwatarwa. Amam kuma a Nijeriya lamarin ba haka yake ba, burin ‘yan siyasa daya ne kawai, su karbi mulki su kuma kare mulkin ko ta halin kaka.
Babban dalilin haka kuma shi ne rashin kyakkyawar akida da kuma rashin bambanta hanyoyin gudanar da mulkin, wannan ne kuma ya haifar da sauye-sauyen sheka da muke fuskanta a fagen siyasar kasar nan a tsawon shekarun da aka yi ana gudanar da mulkin dimokuradiyya.
A yau dimokuradiyyar Nijeriya ta kai shekara 25 da kafuwa, amma irin murnar da aka yi a lokacin da aka dawo da ita a shekara 1999 ya shude saboda yadda ‘yan siyasa suka mayar da hankalinsu kawai wajen neman mulki ko ta halin kaka ba tare da muhimmantar da yi wa al’umma ayyukan raya kasa ba.
Gaba daya ‘yan barandan siyasa sun kwace tsarin dimokuradiyya ta yadda a halin yanzu lamarin mulki ya zama tamkar gado, ba wai wanda ya fi samun yawan kuri’ar al’umma ba.
A tunaninsu, samun kammala mulkin siyasa a karshen wa’adai duk kuwa da kurakuren da aka gani a bayyane ne su ita ce nasarar, kuma ita ce abin da suke tunkaho da su a matsayin nasarorinsu na siyasa.
Tun daga shekarar 1999, tunanin ‘yan siyasarmu duk daya ne, babu bambancin siyasa ko da kuwa sun hade ne ko kuma sun canza suna, tsarin siyasar bai taba canzawa ba har zuwa yanzu.
Amma kuma, ganin an kammala kwamacalar da ke tattare da zaben 2023, a halin yanzu an fara tattaunawar hadewa don samar da gaggarumar jami’iyyar adawa, watakila hakan yana zuwa ne ganin yadda ake zargin cewa, rashin hadin kan ‘yan adawa ya kai samun nasarar jam’iyya mai ci a zaben da ya gabata.
A kan haka, akwai labarai da dama a kafafen sadarwa game da shirin hada kan manyan shugabanin ‘yan adawa, wani abin da suka kasa yi gab da zaben 2023, a yanzu suna shirin kafa wata babbar jam’iyya don su tunkari zabukan shekarar 2027. Domin su tunbuke jam’iyya mai mulki a zabe mai zuwa.
Wannan shirin ba wani abin mamaki ba ne, don a shirye-shiryen zabukkan 2015, manyan shugabannin jam’iyyun adawa sun hade kansu da ya ba su dama suka kafa jam’iyya mai mulki a halin yanzu. Gamayyar ‘yan adawa sun lashe zabe tare da kawar da jam’iyya mai muki daga kan karagar mulki duk kuwa da hasashen da ta yi na yin mulki har na tsawon shekara 60.
Tabbass hankoron kafa gaggarumar jam’iyyar siyasa da ake yi yanzu ya yi kama da wanda aka yi a shekarar 2013.
Bayan bukatar ganin sabbin fuskoki a fagen siyasar, akwai kyakyawar fatan ganin cewa, gamayyar jami’iyyun ‘yan adawa za ta samar wa ‘yan Nijeriya rayuwa tagari ta hanyar ayyukan bunkasa al’umma.
Duk da cewa, akwai zargin rashin cikakkiyar akida a bangaren ‘yan adawan da suke neman hadewa, amma ‘yan Nijeriya sun zaku a samar musu da canji, musanmman ganin ta haka ne za a iya tabbatar musu da romo dimokradiyya.
Haduwar mutanen da suka bayar da gudummawarsu wajen ceto kasar nan daga halin da take ciki, bai zame wa wasu da dama matsala ba, amma kuma bayan gamayyar ‘yan adawar sun ci zabe abubuwa ba su yi wani canzawar da ake bukata ba sai ma dai koma-baya.
A halin yanzu da ake raderadin ana shirin kafa gamayyar manyan jam’iyyu don tunkarar zaben 2027, dole masu wannan shirin su fIto su bayyana wa al’ummar Nijeriya bambancinsu da irin gamayyar da aka yi a baya. Yana da matukar muhimmanci a ga irin kuduri da tanade-tanaden da suke da shi na ceto Nijeriya daga halin da take ciki.
Ya kamata a fahimci cewa, harkokin ‘yan adawa na da matukar muhimmanci in ana son ganin ci gaban tsarin dimokradiyya.
Amma kuma ba kamar yadda al’amarin yake a halin yanzu ba, inda ‘yan adawa suke lami babu wani karsashi na zaburar da masu mulki don su yi wa al’umma ayyukan ci gaba, sun saje tamkar ‘yan jam’iyyau masu mulki.
Domin samun ci gaba, muna fatan samun ‘yan adawa da za su samar da mafita ga irin rashin iya aiki na masu mulki ta hanyar samar da shawarwari masu inganci, da kuma jawo al’umma a cikin tafiyarsu don a iya samar da canjin da ake bukata.
Amma kuma dole mu guje wa yi wa kasarmu fatan sharri don kawai mu samar wa kanmu farin jinin siyasa, ko kuma mu bata masu mulki ba tare da wata hujja ba, wannan ba kishin kasa ba ne.