Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta sake jaddada cewa auren jinsi laifi ne kuma ya saba wa dokar Nijeriya.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani faifan bidiyo na wasu maza guda biyu da suka bayyana junansu a matsayin, ma’aurata.
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Sakataren Majalisar Ministocin Kenya
- Za Mu Dawo Da Martabar PDP A Katsina — Kwamitin Riƙon Ƙwarya
Da yake mayar da martani game da bidiyon, ACP Olumuyiwa Adejobi, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ya ce, “kamar yadda dokar kasa ta Nijeriya ta tanada, an hana aikata irin wadannan laifuka a karkashin sashe na 214 zuwa 217.
“Wannan sashe sun haramta irin wadannan dabi’u na rashin É—a’a irin na dabobbi, kuma har yanzu aikata su haramun ne.
“Kazalika, ya zama wajibi a lura cewa an haramta auren jinsi daya a Nijeriya, dokar hana auren jinsi daya ta shekarar 2014 tana aiki har yanzu.
“Don haka muna jaddada cewar a fahimci abin da wadannan dokoki suka kunsa.
“Muna bukatar hada kai da iyaye wajen yaki da irin wadannan dabi’u kuma duk wanda aka kama ya keta wannan doka, za a hukunta shi.”