Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya koka game da yadda tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Jihar Filato.
Atiku, ya ce rashin daukar matakan da suka dace daga jami’an tsaro ne ke kara ruruwar wutar rikicin.
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Sakataren Majalisar Ministocin Kenya
- Ina Rokon Abba Gida-Gida Ya Dawo APC – Ganduje
LEADERSHIP HAUSA, ta ruwaito cewa rikici ya barke a Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato a farkon makon nan, lamarin da ya kai ga hallaka mutane da dama tare da lalata gidaje da wuraren ibada.
Lamarin ya sanya gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Karamar Hukumar.
Kimanin mazauna kauyuka 30 ne aka kashe a wani kauye da ke Karamar Hukumar da sanyin safiyar Laraba duk da sanya dokar hana fita.
Sai dai kuma da yake mayar da martani game da rikicin, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce ya yi takaicin tashe-tashen hankula da kashe-kashen da aka yi, inda ya bayyana hakan a matsayin cin zarafi kai-tsaye ga zaman lafiya da kuma hadin kai.
Atiku, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter) a ranar Alhamis, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi, musamman idan aka yi la’akari da yawaitar hare-haren ‘yan fashi da makami a Jihar Filato da ma sassan kasar nan.
“Na yi matukar bakin ciki da tashe-tashen hankula da kashe-kashen da aka yi a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato duk da sanya dokar ta-baci ta sa’o’i 24.
“Wannan ta’addanci ne, wanda aka kashe rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba, aka kone gidaje sannan aka jefa mutane cikin hargitsi.
“Ya zama wajibi hukumomin tsaronmu su ba da himma, musamman idan aka yi la’akari da yadda matsalar ‘yan fashin ke ci gaba da faruwa a Filato da sassan kasar nan, rashin sa ido da matakan kariya na iya kara ta’azzara lamarin.
“Ina mika ta’aziyyata ga iyalan wadanda lamarin ya shafa, mu hada karfi da karfe domin ganin ba a sake samun irin wannan rikici ba,” in ji Atiku.