Kwararru a harka sha’anin wutar lantarki sun yi bore ga umarnin karin kudin wutar lantarki na shekara-shekara (MYTO) da hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa (NERC) ta yi, inda lamarin ke ci gaba da janyo muhawara da tayar da kura a tsakanin masu ruwa da tsaki a harka wutar lantarki.
Sabon umarnin na NERCs da ya bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki su 11 damar kara kudin wuta, zai ninka kudin wutar lantarki kan yadda kwastomomi suke biya a baya, a shekarar 2024.
- Tsadar Magunguna Na Barazana Ga Rayukan Majinyata A Nijeriya
- Gwamatin Tarayya Ta Fito Da Tsarin Cin Gajiyar Ma’adanan da Ke Jihar Nasarawa
 A yayin da gwamnati kuma ta dauki nauyin biyan Naira tiriliyan 1.6, kasafin kudin kamfanin lantarki na Nijeriya na shekarar 2024 ya nuna cewa akwai tsarin biyan tallafin naira biliyan 450, lamarin da ke nuni da cewa gwamnati za ta nemo kudi a ciki ko kasuwannin waje.
Masani a bangaren makamashin sun yi gargadin cewa, kara kudin lantarki kai tsaye na nuni ne da cewa za a samu karin farashin abubuwa da karin kudaden kasuwanci, rasa ayyukan yi, hauhawar farashin kayan masarufi da uwa uba kara jefa al’ummar kasa musamman talakawa cikin matsanatsi da kuncin rayuwa.
Wannan karin na zuwa ne yayin da bayanai ke nuni da cewa adadin kwastomomi 51,631 ke amfani da mitar kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 ya zuwa watan Nuwamban 2023.
Yayin da kuma masu amfani da wuta da basu amfani da mitoci suka kai 7,313,039 a cewar NERC.
A cewar hukumar jimillar wadanda suka yi rijista da NESI zuwa Nuwamba, 2023 sun kai 13,112,134, yayin da kuma jimillar kwastomomin da ke da mitoci su 5,799,095, inda adadin amfani da mitocin ya kai kaso 44.23 cikin 100.
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan karin kudin, shugaban kwastamomi na kungiyar NCPN, Kunle Kola Olubiyo, ya yi gargadin cewa karin kudin lantarki zai kai ga janyo hauhawar rashin kayan masarufi da tsadar gudanar da lamura hadi da jefa jama’an kasa cikin kunci mai muni.
Olubiyo ya nace kan cewa mutane da dama sun dogara da wutar lantarki domin neman na kaiwa bakin salati.
Shi kuma a nasa bangaren, manajan gudanarwa na Mainstream Energy Solutions, Audu Lamu, ya ce, zuba tallafin kudin lantarki ba hanyace da ke daurewa ba, kuma hakan na jefa wa masu zuba hannun jari shakkun yin hulda.
A cewarsa, tallafi ba zai bai wa masu zuba hannun jari kwarin guiwa ba, saboda hakan ba zai shawo kan dukkanin matsalolin da harkar ke fuskanta ba.
Shi ma kwararre a bangaren makamashi daga jami’ar Ibadan, Farfesa Adeola Adenikinju, ya ce, tallafi ba zai iya shawo kan matsalolin da suke akwai a bangaren lantarki ba.