Iyalan Al-Kadiriyah na yankin Okekere da ke Ilorin, Jihar Kwara, sun yi kira da a hada karfi da karfe domin ganin an sako wadanda aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan.
Iyalan a yayin da suke murnar sakin ‘ya’yansu mata da masu garkuwa da su suka yi, sun bukaci shugabanin Nijeriya da ‘yan kasar da kada su yi watsi da wadanda har yanzu ake garkuwa da su.
- Tsadar Magunguna Na Barazana Ga Rayukan Majinyata A Nijeriya
- Kofin Afirka 2023: Yadda Manyan Kasashe Ke Tafka Abin Kunya
Biyar daga cikin ’yan uwa mata na ahalin Al-Kadriyar shida da aka yi garkuwa da su a Bwari da ke Abuja a farkon watan Janairu, sun samu ‘yanci.
Haka kuma, wani da aka yi garkuwa da shi, Suleiman Sabo, an kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane a Sauka, daura da titin filin jirgin sama, Abuja.
Jami’an rundunar ‘yansanda da ke yaki da masu garkuwa da mutane a Babban Birnin Tarayya, a kokarin hadin gwiwa tare da sojojin Nijeriya, sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a yankin Zuma 1 da ke Karamar Hukumar Bwari, wadanda aka yi garkuwa da su a ranar 2 ga Janairun 2024.
Da take tabbatar da rahoton, kakakin rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce ‘yansandan sun yi nasarar ceto wadanda lamarin ya rutsa da su a dajin Kajuru a Jihar Kaduna da misalin karfe 11:30 na dare.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, ta hannun daya cikin ahalin Al-Kadiriyah Sherifdeen, sun ce: “A wannan lokacin na murna, kar mu manta da wadanda har yanzu suke fuskantar wahalhalu a hannun ‘yan bindiga, mu ci gaba da yi musu addu’ar Allah ya dawo da su lafiya. Ya zama wajibi mu a matsayinmu na al’umma mu tallafa wa juna da kuma daukaka juna a lokutan da suke shan wahala.”
Sherifdeen ya yi kira da a yi addu’o’in samun lafiya ga rayukan wadanda suka mutu a hannu masu garkuwa da mutane.
Ya kuma mika godiyarsa ga jami’an tsaro, hukumomi, da duk wadanda suka jajirce wajen ganin an ceto ‘ya’ya matan.
Har ila yau, shugaban kungiyar ‘yan asalin Ilorin Masarautar IEDPU na kasa, Alhaji Abdulmumini AbdulMalik, ya sake jaddada bukatar gwamnati a dukkan matakai na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Ya gode wa Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Issa Ali Patanmi da sauran al’ummar Masarautar Ilorin, musamman, don goyon baya da addu’o’in da aka bai wa iyalan Al-Kadiriyah a lokacin da aka bayyana irin manancin halin da suka tsinci kansu.”
LEADERSHIP Hausa ta bayar da rahoton cewa an sace ‘yan matan ne tare da mahaifinsu da kuma wasu mazauna unguwar, inda nan take aka sako mahaifinsu aka umarce su da ya biya kudin fansa kimanin Naira miliyan 60 ga yaran.
Daya daga cikin ‘yan uwa mata mai suna Nabeeha, daga baya masu garkuwa da mutane suka kashe ta saboda ba su biya kudin fansar da gaggawa.
A halin da ake ciki kuma, a yayin aikin ceton, an kama wani da ake zargi mai suna Muhammad Abel, mai shekaru 32, daga Jihar Kogi, tare da kwato bindigar LAR guda daya da harsashi guda goma 10.
A jiya kuma aka samu rahoton an sako wasu mutum bakwai da aka yi garkuwa da su a rukunin gidajen Sagwari da ke Karamar Hukumar Bwari a Babban Birnin Tarayya Abuja.
An sace su ne kwanaki da suka wuce lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki a gidan da misalin karfe 8 na dare
Wata daga cikin wadanda abin ya shafa, Talatu Salihu, daliba mai matakin digiri na 500 akan Laburare da Kimiyyar Yada Labarai, Jami’ar Bayero Kano (BUK)