Wannan shine kuma karshen maudu’in da aka yi mako biyar ana magana akan shi, da yardar Allah kuma mako mai zuwa wani sabon maudu’i ne za mu fara da shi mai suna “Gudunmawar da makarantu ke yi wa al’umma”.
17.Dogara a kan wasu
Dogara a kan wasu wani babban al’amari ne wanda dalibai suka cika dogara da shi,haka abin yake dalibai wadanda suka ta’allaka da wasu su samu cin jarrabawa babu yadda za ayi su yi karatu domin su shiryawa fuskantar jarrabawa.
Mafita
Ka yarda da kanka ka yi karatu sosai domin ka samu nasarar cin jarabawa, ka yi kokari kada ka dogara a kan wasu saboda babu wanda za a iya amince masa a dakin jarabawa.
18.Rashin yarda da kai
Yadda ka ke ji cikin ranka da yadda fuskantar shiga cikin mawuyacin hali wasu abubuwa ne da suke nuna ko zaka iya tafiya daidai da yadda ka samu kanka ko kuma akasin haka.
Bugu da kari wadanda basu da tabbacin irin shirin da suka yin a fusaknatar jarabawa, su kan kasance basu wani tabbas.
Rashin tabbas na inda dalibi ya fuskanta wato yadda shi dalibin yake ganin ya shirya fuskantar jarabawa, wannan ma yana fuskantar irin kokarin da zai yi idan lokacin jarabawa ya yi.
Abin da aka fi so shi ne a matsayinka na dalibi sai ka yi kokari kada ka sa wa jikinka kasala ka dage da kasancewa kana da babbar fata ta samun nasara a jarabawar da zaka yi.
Mafita
Ka yarda da cewar kai ma zaka iya yin duk yadda wani yake domin cin jarabwa kana da yadda, kana da yadda zaka yi said ai idan baka dam aba, don haka abin ba wanda za ka yi wasa da shi bane dagwa zaka yi.
19 Rashin mai da hanakali na dalibai
Wannan shine babban abinda yake taimakawa wajen faduwar jarabawa ta dalibai wato al’amarin daya shafi rashin maida hankal ga karatu, saboda wasu daliban suna bari ne sai ranar da za su rubuta jarabawar ce za su nemi yinkaratun bayan ba a fafe gora ranar tafiya.
Duk dalibin da yake yin haka ya kwana da sanin cewar kan shi ne kadai yake cut aba kowa ba,domin wannan ya yi matukar nunawa a fili akwai rashin maida hankali da rashin sanin ciwon kai.
Tun da ka san abinda ya dace kayi domin jarabawa ce ka ke fuskanta sai ka shirya yadda zaka rubuta amsoshin tambayoyin da da ake yi maka dayin hakan zai kai ga sawa ka samun yin nasara.
Mafita
Ka yi kokari ka guji ma duk wani abinda kake ganin zai samar maka matsala ka yi abubuwan da suka kamata kafin ranarrubuta jarabawar ta zo.
- Rashin wani buri na wani abu da dalibi ke son yi a rayuwa
Sauran dalilin da ya sa dalibai suke faduwa jarabawa shi ne saboda basu da wata manufa ko aniya,tare da abinda suke son su zama a gaba bayan sun kammala makaranta, don haka shi yasa ita maganar karatu suna dai yi ne domin kar ace ba suyi bugu da kari kuma abin bai shiga zuciyarsu ba.Yin hakan shi ke taimakawa wajen faduwa jarabawa, said ai kuma yana da matukar kyau ace dalibi yana da wata manufa ta shi da yake son cimmawa a gaba domin hakan zai taimaka kwarai matuka,idan har ta kasance dalibiu bai da wani burin zama wani abu rayuwa yin hakan ba zai taimakawa kan shi domin bai niyyar haka a rayuwarsa. Shi ke sa daliba ya kasance ya gaji bai wata laka ta son yin karatu domin babu takamaiman wani abinda aka gaba na rayuwa.
Mafita
Sai ayi kokari wajen tunanin abinda ya dace ayi wannan kuma ana fara yin haka ne tanyar taimako da Iyaye suke badawa wajen bunkasa karatun ‘ya’yansu,ta hanyar taimaka masu wajen agniun sai sun cimma burinsu na abinda suke son zama a gaba. Ana ganin hakan wajen ‘ya’ya lokacin suna yara kanana za a lura da nau’in wasannin da suke yi,idan ana matukara lura dasu hakan zai taimaka.