Kwamishinan lafiya ta jihar Kaduna, Umma K. Ahmed, ta bayyana cewa sama da mutane miliyan 5 a jihar na fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka na yanayi da ake sakaci da su (NTDs) da suka hada da makanta da elephantiasis da dai sauransu.
Ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da take ganawa da manema labarai domin bikin ranar yaki da cututtuka da ake sakaci da su, NTDs na duniya na shekarar 2024 a Kaduna.
- Xi Ya Tayawa Azali Assoumani Murnar Sake Zaben Shugaban Comoros Ta Wayar Tarho
- Micheal Keating: Kasar Sin Ba Barazanar Tattalin Arziki Ba Ce
A cewarta, Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta kebe kowace ranar 30 ga watan Janairu, domin “fadakar da dukkan al’ummomin duniya kan illar NTDs, wanda ke shafar sama da mutane biliyan daya a fadin duniya, inda kusan kasashe 149 ke fuskantar wadannan cututtuka. kuma Afirka tana dauke da kusan rabin wannan cutar.”
“Nijeriya ita ce kasa ta biyu da ke da damuwa da illar NTDs a duniya, kuma itace a gaba wurin fama da barazanar cutar a Afirka da ke da mutane fiye da miliyan 120 da ke rayuwa a cikin hadarin kamuwa da cututtuka da ake sakaci ko watsi da su.
“A jihar Kaduna, mutane 5,970,722 na fuskantar barazanar kamowa da cutar makanta, tsutsar ciki, filariasis lymphatic da bilharziasis” inji kwamishinar
Jihar Kaduna dai tana hada kai da duk masu ruwa da tsaki musamman kungiyoyin raya kasa masu zaman kansu (NGDOs) irin su Sightsavers, wajen bada goyon baya wurin magance matsalar NTDs a jihar Kaduna.
“Na yi matukar farin cikin bayar da rahoton cewa an samu gagarumin ci gaba cikin shekaru 10 da suka gabata, wanda hakan ya nuna mun samu nasarar dakile yaduwar cutar onchocerciasis a kananan hukumomi 16 da kuma kawar da cutar trachoma a jihar Kaduna, kamar yadda rahoton binciken cutar Trachoma ya nuna na 2023.
“Sauran nasarorin da ma’aikatar ta samu sun hada da kashe tsutsotsin ciki da ke barazana ga kananan yara da kuma raba Magungunan cutar Lymphatic Filariasis da Schistosomiasis masu yawa a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.
“An horar da ma’aikatan kiwon lafiya 834 kan tantancewa da kula da cututtukan NTDs, an horar da malamai 3,502, da kuma mutane 10,249 don rarraba magunguna a tsakanin al’ummarsu a shekarar 2023.
“Ina so in sanar da ku duka cewa, jihar Kaduna ta himmatu wajen kara kaimi domin cimma burin hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya na kawar da barazanar cutar NTDs nan da shekarar 2030 tare da ba da gudummawa ga ingantaccen tsarin kiwon lafiya ta hanyar inganta iya aiki, hada kan al’umma tare, da bayar da gudummawar kiwon lafiya na duniya baki daya.”