‘Yan Nijeriya da dama na ci gaba da nuna damuwarsu kan yawaitar jabun magunguna da abubuwan sha da kayan abinci da sauran kayayyaki a kasar.
Kan haka ne Suka bukaci hukumomin da abin ya shafa su fara gudanar da wani cikakken bincike na kasa kan lamarin da kuma hanzarta sauya yanayin don kauce wa tabarbarewar yanayin kiwon lafiya da sauran abubuwan da ke faruwa.
- Za Mu Ci Gaba Da Aiwatar Da Abubuwan Da Suka Sa LEADERSHIP Ta Karrama Mu – Gerawa
- Xi Ya Taya Nangolo Mbumba Murnar Zama Shugaban Kasar Namibiya
Sakamakon binciken ma’aikatar hako ma’adanai da LEADERSHIP ta gano ya nuna cewa magunguna marasa inganci ne ke haddasa mutuwar mutane 500,000 duk shekara a yankin Kudu da hamadar Sahara.
Rahoton ya kuma nuna cewa, kusan mutum 267,000 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon amfani da jabun magungunan zazzabin cizon sauro da marasa inganci.
Mutane da dama sun shiga shafukan intanet don yin kira ga Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) da ta gudanar da bincike tare da fitar da ingantattun matakan da za a bi don magance yawaitar jabun kayayyakin a kasuwannin NIjeriya.
Wani dan kasuwa a sananniyar kasuwar Utako da ke Abuja, Ugochukwu Henry, ya ce rahoton ya shafi harkokin kasuwanci, amma hakan bai hana mutane sayen kayayyaki a kasuwar ba.
Wata kwastoma a kasuwar, Ruth Ode, ta ce halin da ake ciki matsin tattalin arzikin kasar ne ke haddasa wannan barazana.
Wani kwararre a fannin lafiya ya ce akwai bukatar a kara kwantar da hankulan mutanen da abin ya shafa domin hakan na iya haifar da annoba.
Kwararru sun shaida wa LEADERSHIP cewa yawaitar jabun kayayyaki da marasa inganci a kasuwannin Nijeriya da dama, tare da amfani da su na haifar da karuwar mace-mace a kasar.
Suka ce yawaitar magungunan jabu cin zarafi ne ga masana’antar kiwon lafiya ta kasar, inda suka bayyana cewa hakan na haifar da asarar rayuka da kuma raunana kwarin gwiwa kan magunguna, da ma’aikatan kiwon lafiya, da ma daukacin tsarin kiwon lafiya.
Mafi yawan jabun kayayyakin abinci a Nijeriya
Bincike ya nuna cewa kayan abinci na jabu da aka fi yawaita yi a Nijeriya sun hada da jabun magunguna, shinkafa jabu, gurbataccen man kayan lambu, jabun barasa da kayan abinci da kwanankin watan amfani da su suka kare da kuma marasa inganci.
Wadannan samfuran ba koyaushe suke cika ka’idojin aminci da inganci ba, suna haifar da hadari ga masu amfani da su.
A watan da ya gabata ne Hukumar Kula da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa (NAFDAC) ta gano wasu jabun kayayyaki a kasuwar Ezukwu (Cemetery Market) dake garin Aba, Jihar Abia.
Hakan ya jawo martani daga masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya.
Shiga tsakanin da hukumar NAFDAC ta yi ya kai ga kwace kusan kayayyakin da kwanakin watansu ya kare 2000, da suka hada da barasa, abubuwan sha, da sauran abubuwan da suka kare. Wannan matakin ya yi sanadin rufe shaguna sama da 240 da ke aiki a matsayin masana’antu, da kera kayayyaki, da sake gyarawa, da kuma sayar da kayayyakin jabu cikin rashin tsafta, a cewar sanarwar da hukumar abinci ta fitar.
Tasirin jabun abinci ga tattalin arziki
Bayan hadarin lafiya, samfuran kayan jabu suna kuma haifar da illa ga tattalin arziki.
Wani kiyasi na PricewaterhouseCoopers (PwC) ya nuna cewa Nijeriya na yin asarar kusan Naira biliyan 200 a duk shekara saboda jabun magunguna, ban da magunguna marasa inganci.
A cewar wata kungiya mai zaman kanta, HealthWise International, kididdige madaidaicin tasirin tattalin arziki yana da kalubale; samarwa da rarraba kayan abinci na jabu na iya samun illa mai yawa a duka matakan tattalin arziki wato ‘macroeconomic’ da wadanda suka hada da: kashe kudi akan kiwon lafiya, raguwar yawan aiki, lalata amincin mabukaci, rage yawan amfanin gona, karkatar da albarkatu, hauhawar farashin, tasiri akan kananan sana’o’i, da bambancin zamantakewa da tattalin arziki da sauransu.
Dabarun yakar barazanar dake tunkarowa
Masana sun bukaci gwamnati da ta karfafa tsarin mulki, kara dubawa da sa ido, hada kai da masu ruwa da tsaki a masana’antu; kaddamar da yakin wayar da kan jama’a don ilmantar da masu amfani da irin wadannan kayayyaki game da hadarin da ke tattare da abincin jabu da kuma yadda za a gane su; ingantawa da kuma ganowa.
Bayar da horo kan don gane nau’in jabun kayan abinci
Pharmacare, wata kungiya ce mai fafutuka kan tabbatar da magungunan gaskiya, ta jero wasu shawarwari da za su taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen gano abubuwa na abincin jabu.
Bincika alamomi da mazubi. Gano kurakuran harufan da aka rubuta sunan magani ko abinci, haruffan da ba a saba gani a jikin kayan ba, ko rashin ingancin rubutu akan murfi. Bincika mazubi da duba alamun tambari, Tabbatar da dacewar bayanin mazubi shin ya ya dace da samfurin ciki, da sauransu
1. Gano lokacin da kwanan watan amfani da kaya zai kare
2. Ku yi amfani da hankalinku wajen gano kamshi, dandano, da kamannin kaya. Idan kamshi ko dandano na samfurin abinci ya saba da irin wanda kuke ci, to zai fi kyau a guje shi. ku yi hankali da sinadari mai tsananin karfi ko kamshi, kawai ya kamata ka sayi kaya daga mashahuran dillalai.
A Bude Rumbunan Abinci —Majalisa
Majalisar Wakilai ta nemi gwamnatin tarayya ta dauki matakan ganin an kawo kareshen tsadar abincin da ake fuskanta a sassan kasar nan, ‘yan majalisar sun bayyana haka ne a ganawarsu da ministan kudi Wale Edu da ministan Kaszafin kudi Atiku Abnubakar da kuma ganmna babban bankin Nijeriya Olayemi Carsosor, inda suka nemi bayanai a kan tabarbarewar tattalin arzikin kasa da kuma tsafdar rayuwa da al’ummar Nijeriya kem fuskanta.
A kan haka suka nbukaci wgamnati ta fito abinci da aka adana don kota kwana na sassan kasar nan don a sayar wa al’umma a farashi mai rahusa.
Za mu shawo kan lamarin – Gwamnati
A nasa martanin ta gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, tana daukar dukkan matakan da suka kamata na ganin an shawo kan matsalar tsafdar abinci da ta addabi al’umma, kwamiti na musamman na shugaban kasa a kan mastalar abinci ya bayyana cewa, an fara daukar matakan ganin karshen mastalar, cikin matakan sun hada da fitar da abincin da aka ajiye, za a fitar don a sayar wa al’umma a cikin farashi mai rahusa, Miniatan yada kanbarai, Mohammed Idris ya sanar da haka. Ya kuma ce, wgamnati ta damu da zanga zangar tsadar rayuwa da aka yi a wasu sassan Nijeriya.
Cin Hanci Da Rashawa Ne Silar Matsalar – Dattawan Arewa
Ita kuwa kungiyar dattawan arewa ta nuna damuwarta ne a kan hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya, ta ce in har ba a dauki matakin da ya kamata ba zai iya haifar wa da al’umma babbar matsalar rayuwa.
Jami’in watsa labarai na kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya sanar da haka, ya ce, dole a dauki jin dadin al’umma da muhimmanci in ana so a zauna lafiya. Ya kuma ce dole gwamnati ta dauki matakin yaki da cin hanci da rashawa wanda sune silar dukkan matsalar da ake fuskanta.