A ranar Talata ne majalisar wakilai ta sanar da fara zango na biyu na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan mastalar tattalin arzikin da Nijeriya ke fuskanta tare da nemo hanyoyin magance tsadar rayuwa da al’umma ke dandanawa.
Bayanin haka ya fito ne daga mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi. Ya ce, tattaunawar zai tattaro masu ruwa da tsaki a bangaren tattalin arzikin kasa kamar, Ministan Kudi, Minsitan kasafin Kudi da tsare- tsare da gwamnan Babban Bankin Nijeriya da kuma shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin haraji.
- Shirin Gwamnati Na Samar Da Mafi Karancin Albashi
- Kungiyar ‘Yan Dangwale Ta Nemi Majalisa Ta Tsige Sarakunan Kano 5 Da Dawo Da Sanusi
Babban sakataren majalisar wakilai, Yahaya Danzaria, ya tabbatar da wannan labarin a wata sanarwar da ya sanyawa hannu aka kumam raba a manema labarai a Abuja.
Majalisar ta fara irin wannan tataunawar ne a watan Nuwamba na shekarar 2023, inda ta tattauna da bangaren jami’an tsaro.
Shirin tattaunawar da masu ruwa da tsaki, shiri ne da Shugaban Majalisar wakilai Abbass Tajudeen ya bullo da shi don karfafa tafiyar da gwamnati ta hanyar tafiya da al’umma tare da kuma sa ido a kan yadda ake kashe kudaden gwamnati.
Wannan na daga cikin aikin majalisa na sanya ido a kan yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke tafiyar da harkokinsu, hakan kuma zai karfafa dangantakar da ek a tsakanin bangaren zartawa da kuma na majalisa masu yin dokoki.
A lokacin da majalisar ta dawo aiki bayan hutun karshen shekara, shugaban majalisa, Tajudeen ya lura da yadda tattalin arziki kasa ya tabarbare, a kan haka ya nemi a tattauna da hukumomi da ma’aikatun da ke kula da bangaren tattalin arziki don nemo hanyoyin kawo karshen matsalolin da ake fuskanta.