Kwamitin sulhu na MDD ya kada kuri’a game da daftarin kudurin tsagaita wuta a Gaza nan da nan, wanda kasar Aljeriya ta gabatar a madadin kasashen Larabawa, to sai kuma ba a zartas da kudurin ba sakamakon kuri’ar kin amincewar da Amurka ta jefa.
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya jefa kuri’ar amincewa da kudurin, kana ya ba da jawabi don bayyana matsayin bangaren Sin. Zhang Jun ya ce bangaren Sin ya yi bakin ciki sosai game da yadda Amurka ta ki amincewa da daftarin.
- Cibyar Dakon Kaya Da Kasar Sin Ta Gina Na Taimakawa Bunkasar Kayayyakin Da Ake Fitarwa A Kasar Uganda
- Don Tabbatar Da Adalci A Duniya Ana Bukatar Hadin Gwiwar “Global South”
Daftarin kudurin da Aljeriya ta gabatar a madadin kasashen Larabawa, na bukatar tsagaita wuta a Gaza nan da nan, da saki dukkan mutanen da ake tsare da su, da shigar da kayayyakin jin kai, da kuma hana tilastawa jama’a canja matsuguni, wannan ba ma kawai bukata ce ta gaggawa game da yanayin da ake ciki a yanzu ba ne, har ma yana da alaka da samar da abubuwan bukatun jin kai, don haka ya kamata dukkan mambobin kwamitin sulhun su nuna goyon baya ga kudurin.
Sakamakon jefa kuri’un ya nuna cewa, kwamitin sulhun MDD ya cimma matsaya guda daya kan batun, amma Amurka ta rushe matsayar. Ya ce matakin na Amurka ya jefa Gaza cikin yanayi mai hadari.
A yayin jefa kuri’ar ta wannan karo, daftarin kudurin da Aljeriya ta gabatar ya samu kuri’un amincewa 13, ciki har da kuri’ar kasar Sin, yayin da Birtaniya ta janye jiki daga jefa kuri’a.
Game da batun, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labaru yau Laraba cewa, Amurka ta sake yin fatali da daftarin kudurin kwamitin sulhu na MDD kan zirin Gaza, lamarin da ya sa al’ummar Gaza cikin wani yanayi mai hadari.
Da take karin haske kan wannan tambaya, Mao Ning ta yi nuni da cewa, halin da ake ciki na jin kai a Gaza, yana da matukar muni, kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin ya yi tasiri sosai. Tilas ne kwamitin sulhun ya dauki matakai cikin gaggawa don inganta tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen yakin.
Mao ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da dukkan bangarori na kasa da kasa, wajen ingiza kwamitin sulhu na MDD ya dauki matakan da suka dace, da yin kokarin kawo karshen yakin Gaza nan da nan, da sassauta yanayin jin kai, da sa kaimi ga aiwatar da shirin kafa kasashe biyu da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na dogon lokaci a yankin Gabas ta Tsakiya. (Ibrahim Yaya, Safiyah Ma)