Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin, Kemi Nanna Nandap, a matsayin Kwanturola-Janar ta Hukumar Kula da shige da fice ta kasa (NIS).
Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), ya ce nadin ya fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2024.
- Tinubu Ba Zai Yi Murabus Ba, inji Ministan Yaɗa Labarai
- Da Dumi-Dumi: An Samu Sauyin Shugabanci A Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa
“DCG Nandap za ta karbi mulki daga hannun Misis Caroline Wura-Ola Adepoju, wacce wa’adinta zai kare a ranar 29 ga Fabrairu, 2024.
“Kafin nadinta a matsayin Kwanturola-Janar, Nandap ta kasance mataimakiyar Kwanturola-Janar mai kula da ‘yan gudu hijira ta ma’aikatar.