Sanata Kashim Shettima mutum ne mai matukar basira, kuma kwararre, kana dan siyasa ne wanda ya lakanci magana a lokacin da ya dace cike da fasaha, wanda kuma dan asalin kabilar Kanuri ne.
Sanata Shettima mutum ne wanda aka sanshi da iya mu’amala, yana da raha kuma ba ya fushi, sannan ba ya nuna kyama da wariya ga kowane bangare.
A lokacin da Kashim Shettima yake gwamnan jihar Borno (2011-2019) domin tabbatar da rashin nuna wariya da hadin-kan kasa, ya yi bajintar jawo kowane bangare a mulkinsa, wanda ya dauki mataimaka masu ba shi shawara wanda ya hada da dan kabilar Ibo kuma Kirista daga jihar Anambra, daya dan kabilar Urhobo Kirista daga jihar Delta, hadi da daya Kirista dan asalin jihar Edo, daya Bayarabe shima Kirista, sannan da daya Bafulatani daga jihar Gombe tare da daya Bahaushe daga jihar Zamfara.
An haifi Sanata Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno ranar 2 ga watan Satumban 1966 a birnin Maiduguri, ta jihar Borno, da ke Arewa Maso Gabashin Nijeriya, wanda ya fito ne daga zuriyar marigayi Sir Kashim Ibrahim. Wanda daga bisani ya auri matarsa, Uwargida Nana Shettima, suna da ‘ya’ya uku, mata biyu da namiji daya.
Sanata Shettima ya fara karatun sa na firamari a Lamisula Primary School dake Maiduguri a 1972 zuwa 1978; sai Gobernment Community Secondary School, dake garin Biu a kudancin jihar tsakanin 1978 zuwa 1980; wanda daga bisani aka koma Gobernment Science Secondary School, Potiskum a jihar Yobe (makobciyar jihar Borno) wanda nan ya kammala karatun sa na sakandire a 1983. Sanata Kashim ya tafi Jami’ar Maiduguri inda ya yi digirinsa (BSc) kan Agricultural Economics a 1989. Sannan da aikin yiwa kasa hidima (NYSC) a Bankin ‘Nigerian Agricultural Cooperatibe Bank’, a Calabar na jihar Cross Riber a 1989-1990.
Haka zalika, ya samu digirinsa na biyu (MSc) kan Agricultural Economics a 1991, a Jami’ar Ibadan. Sannan daga baya Shettima ya fara aikin Malanta a Jami’ar Maiduguri a tsangayar Agricultural Economics tsakanin 1991 zuwa 1993.
A shekarar 1993, Kashim ya mazaya zuwa aikin banki, inda ya fara aiki da rusasshen bankin ‘Commercial Bank of Africa Limited’ a matsayin babban akanta zuwa Manajan Bankin, a cibiyar bankin da ke unguwar Ikeja, a jihar Lagos.
A shekarar 2001, Shettima ya kowa aiki da Zenith Bank a matsayin shugaban reshen bankin a Maiduguri, kuma ya rike Babban manaja a bankin zuwa mataimakin Janar Manajan yankin Arewa Maso Gabas kafin daga bisani ya ajiye mukamin sa na Janar Manajan Bankin a 2007, sakamakon nada shi Kwamishinan kudi da ci gaban tattalin arziki na jihar Borno, kana kuma ya rike mukamin Kwamishina a ma’aikatu 5; a ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu, na ma’aikatar ilimi, na ma’aikatar aikin gona tare da na ma’aikatar kiyon lafiya a lokacin tsohon Gwamnan jihar, Sanata Ali Modu Sheriff.
A zaben fid-da-gwanin jam’iyyar ANPP na watan Junairun 2011, an zabi Engineer Modu Fannami Gubio a matsayin dan takarar Gwamnan jihar Borno, wanda daga bisani wasu mahara suka kashe shi, a sa’ilin da Shettima shi ne ya zo na biyu a zaben fid-da-gwanin tare da maye-gurbinsa da marigayin. A zaben 26 ga April 2011, Kashim Shettima ya lashe zaben da kuri’u 531,147 wanda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Muhammed Goni, da kuri’u 450,140.
Sanata Kashim ya sake lashe zaben gwamnan jihar a 2015 a karkashin jam’iyyar APC, yayin da kuma aka zabe shi matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya 19. Wanda ya yi amfani da wannan dama ta jan akalar kungiyar gwamnonin wajen samar da hadin kan Arewacin Nijeriya hadi da yunkurin sake farfado da masana’antun da yankin ya mallaka wadanda ke fuskantar barazanar durkushewa.
Duk da irin kalubalen da jihar Borno ta fuskanta sakamakon tabarbarewar tsaron da kungiyar Boko Haram ya haifar wanda ya fara a 2011, gwamna Kashim Shettima ya taka rawar gani wajen gudanar da mulkin jihar. Yayin da Mai Baiwa Shugaban Kasa shawara ta fuskar tsaro da Hafsan Sojojin Nijeriya duk yan asalin jihar ne, kana da irin yadda gwamnatin tarayya ta sahale masa damar daukar matasa Yan Cibilian JTF a 2013.
Aikin sa-kai na Yan Cibilian JTF ya taimaka ainun wajen taimakon Sojojin Nijeriya a yakin da suke yi da mayakan kungiyar Boko Haram. Al’amarin da ya dada karsashin gwamnatin Shettima wajen saya wa yan cibilian JTF motoci da kayan yaki, kayan alatu da alawus a kokarin da suka nuna wajen goyon bayan sojojin.
Sanata Kashim Shettima ya taka muhimmiyar rawa wajen bayar da cikakken goyon baya ga Sojojin Nijeriya hadi da sauran jami’in tsaro a lokacin yaki da matsalar tsaro Boko Haram, wanda idan ba a manta ba, a September 2014, tabarbarewar tsaron ta yi kamari a birnin Maiduguri, da jihar Borno baki daya inda mayakan suka mamaye kananan hukumomi 20 a cikin 27 a jihar, al’amarin da ya tilasta wa jama’a kauracewa garuruwansu da jihar baki daya; kafin daga bisani Sojojin Nijeriya su fatattake su tsakanin 2015-2016. Amma domin bai wa jama’a kwarin gwiwa, a tsakiyar wannan halin, Gwamna Kashim Shettima ya dawo Maiduguri tare da gangami na musamman domin kare martabar jihar.
Bugu da kari kuma, gwamna Kashim Shettima ya daura damarar inganta rayuwar al’ummar da rikicin Boki Haram ya rutsa da su ta hanyar samar muhallin wucin-gadi da gyara wadansu domin tsugunnar da jama’a. Wanda daga baya gwamnatin sa ta fito da ingantaccen shiri na musamman domin sake farfado da yankunan da rikicin ya shafa a jihar, yayin da aka samu gagarumar nasara tare da sake tsugunnar da jama’a. Haka kuma Kashim Shettima ya dukufa wajen sauya fasalin harkokin ilimi tare da bunkasa makarantun firamari da sakandire a jihar hadi da na kwana domin bai wa marayu kimanin 50, 000 wadanda suka rasa mahaifa sakamakon matsalar tsaro a fadin jihar.
Biyo bayan jajircewa da kwazon gwamna Kashim Shettima ya jawo masa tagomashi da mambobin yabo a ciki da wajen Nijeriya. A 2014 ne Gwamna Shettima ya lashe kambin gwarzon gwamna na shekara a kamfanin Jaridar Leadership, Gwarzon Gwamna Na Shekarar 2015, na Uwar Kungiyar Yan Jaridu ta kasa (NUJ); Gwarzon Gwamnan Shekarar 2015 na NewsWatchTimes Newspapers, Gwarzon Gwamnan Shekarar 2015 na Jaridar Banguard Newspapers; Gwarzon Gwamnan Shekarar 2016 na Mujjalar Tell Magazine kuma wanda ya lashe kautar lambar yabo ta 2017 (Zik Prize) ga shugabani; kana da lambar yabo ta ‘Kaduna NUJ Award’ ta 2017, da FCT NUJ Merit Award a 2017.
Har wala yau, kafin ayyana shi a matsayin Mataimakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi a wannan makon, Sanata Kashim Shettima shi ne Sanata mai wakilatar jihar Borno ta tsakiyar a majalisar dattawan Nijeriya, a zaben 2019 da ya gabata.