Fadar Shugaban Kasa, ta bayyana cewar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), ba ta dage haramcin bai wa ‘yan Nijeriya biza ba.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa kan harkokin hada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X da yammacin Talata.
- Za A Fara Amfani Da Kimiyyar Zamani Wajen Yaƙar ‘Yan Bindiga – Ministan Tsaro
- Ana Kokarin Rantsar Da ‘Yan APC 16 A Majalisar Filato Ta Barauniyar Hanya – Gwamnatin Jihar
Bayo ya ce UAE ba ta koma bai wa ‘yan Nijeriya biza ba.
Tun da farko dai wasu rahoatanni sun ruwaito cewa Dubai ta dage haramcin biza kan Nijeriya, sai dai Onanuga ya yi watsi da rahotannin.
“Bayanai da ke yawo kan cewa Dubai ta koma bai wa ‘yan Nijeriya biza ba gaskiya ba ne.
“Bayanin ba daga gwamnatin Nijeriya ko UAE suka fito ba,” in ji Onanuga.
A watan Oktoban 2023 ne, Dubai ta haramta wa ‘yan Nijeriya tare da wasu ‘yan kasashe 19 daga Nahiyar Afrika shiga kasarta.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Dubai ke kakabawa kasashe irin wannan takunkumi ba.