Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya amince da biyan tallafin karin albashin Naira 20,000 ga dukkan ma’aikatan jihar.
Gwamnan ya aiwatar da shirin ne biyo bayan rokon da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa gwamnatocin jihohi na su aiwatar da shirin biyan tallafin albashin ma’aikata domin rage musu wahalhalu da tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.
- Tinubu Da IBB Sun Yi Ganawar Sirri A Neja
- Mahaifin Matar Gwamnan Neja, Sarkin Malami Nupe Ya Rasu Yana Da Shekaru 90
In ba a manta ba, mun rahoto muku a ziyarar da shugaban kasa ya kai jihar Neja cewa, ya roki gwamnonin jihohin da su fara biyan tallafin albashin ma’aikata har zuwa lokacin da za a fitar da mafi karancin albashi.
Gwamna Bago ya sanar da fara biyan tallafin albashin ne na N20,000 a zaman majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin da ke Minna a ranar Laraba.
Gwamna Bago ya bayar da tabbacin cewa, za a gaggauta biyan kudin, inda ake sa ran ma’aikatan za su fara karbar kudadensu tun daga ranar Laraba.