ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dokar Hana Sayar Da Burodi Mara Shaida, Litar Mai Fiye Da 50 Ta Tabbata A Zamfara, Gwamna Dauda Ya Sa Hannu

by Leadership Hausa
2 years ago
zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu a kan dokar da ta haramta sayar da burodin da ba a liƙa takardar shaidar inda ake yin sa ba, tare da jigilar sa a buhu.

Haka kuma an haramta sayar da man fetur fiye da lita 50, haka ma an haramta motoci masu gilashi mai duhu a duk faɗin jihar Zamfara.

Sojoji Sun Ceto Mutane 10 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Zamfara

ADVERTISEMENT

Dokar Hana Sayar Da Burodi Mara Shaida, Litar Mai Fiye Da 50 Ta Tabbata A Zamfara, Gwamna Dauda Ya Sa Hannu

A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ta ce dokar mai lamba 02 da mai lamba ta 04, 2024 za ta taimaka wajen magance wasu matsalolin da ke taimakawa ga matsalar tsaro a jihar. Jiya Talata ne Gwamnan ya sanya hannu a dokar a gidan gwamnatin jihar da Gusau

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Kakain Gwamnan ya ce, an sanya dokar ne sakamakon hare-haren da ake kai wa wasu al’ummomi a sassan jihar.

“Sakamakon hare-haren da aka kai wa al’ummomin wasu Ƙananan Hukumomin jihar nan, musamman Zurmi, Shinkafi, Ƙaura Namoda da Talata Mafara, tare da samun ƙaruwar kai hare-hare da sace mutane a wasu yankuna da manyan hanyoyin jihar.

“Gwamna Lawal ya sanya hannu a dokar No. 02 2024, wacce ta haramta sayar da biredi mara takardar shaida, tare da sanya biredin a buhuna, an kuma haramta wasu ayyukan da ba a amince da su ba a jihar.

“Wajibi ne duk gidajen biredi su sanya takarda mai ɗauke da cikakken adireshin kamfanin, tare da bayanan ayyukan da su ke aiwatarwa, ana so su yi wannan cikin gaggawa.

“Kada wani gidan man fetur ya kuskura ya sayar da fiye da lita 50 ga kowace mota a lokaci guda. Daga yanzu kuma, gidajen mai za su sayar da mai ne tsakanin ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

“Sayarwa ko yawo da biredi, yanzu zai zama kawai a Hedikwatar kowace Ƙaramar Hukuma: Amma a Gusau, an amince a sayar a yankunan: Hanyar Damba—Zaria; Gada Biyu—Sokoto; Command Guest House a hanyar Ƙaura Namoda; Gusau Garage—Dansadau.”

Haka kuma dokar ta No. 04, 2024, wacce Gwamnan ya sanya wa hannu, ta haramta motoci masu ɗauke da gilashi mai duhu a Zamfara. “Haka kuma an haramta wa masu motoci rufe lambar motocin su a yayin da suke tafiya.

“Wajibi ne duk masu motoci su kasance tare da cikakkun takardunsu, sannan su bi dokar kiyaye dokokin hanya ta jihar Zamfara mai lamba No. 2, 2015, ko duk wata doka da ta shafi wannan.”

zamfara
Leadership Hausa
+ postsBio
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Kamfanin Huawei Ya Horas Da Matasa 241 A Arewacin Uganda

Kamfanin Huawei Ya Horas Da Matasa 241 A Arewacin Uganda

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.