Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya (SSANU) ta sanar da kawo karshen yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, domin bai wa gwamnati damar yin abin da ya kamata.
Shugaban kungiyar, Mohammed Ibrahim, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki, wanda kungiyar marubutan ilimi ta Nijeriya (EWAN) ta shirya ranar Lahadi a Legas.
- Yadda Kungiyar SSANU Da NASU Suka Gudanar Da Zanga-zangar Lumana A Zariya
- Yajin Aikin ASUU: Malamin Jami’a Ya Yi Barazanar Ajiye Aiki Kan Rashin Albashi
Taron wanda ya samu halartar shugaban kungiyar ma’aikatan da ba masu koyarwa ba (NASU), Mista Ibeji Nwokoma, yajin aikin wanda aka yi kan rashin bashin albashi da ma’aikatan ke bi.
Idan za a iya tunawa, kwamitin hadin guiwa na kungiyoyin kwadago na jami’o’in da abin ya shafa, a ranar 18 ga watan Maris, ya umarci mambobin kungiyar da su tsunduma yajin aikin gargadi kan hana su albashi na watanni hudu da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya a shekarar 2009.
“Mun yi taro da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja a ranar Laraba kuma babu wani abu da a zahiri da ya fito dangane da batun.
“Eh, sun yarda da cewa muna yajin aikin ne kuma matakin ya gurgunta ayyukan da ake yi a harabar jami’o’in tarayya.
“Don haka taron ba komai ba ne illa neman a dakatar da yajin aikin, yayin da suka gaza yin wani abu cikin gaggawa.
“Za a kawo karshen yajin aikin da karfe 12 na dare. Za mu koma rassanmu daban-daban domin duba sakamakon yajin aikin gargadin, da kuma taron da aka yi da gwamnatin tarayya a baya-bayan nan, daga nan kuma za mu yi duba kan mataki na gaba.” Cewar Ibrahim