Gwamnatin Tarayya ta ce ta gayyaci Malamin addinin Musulunci na Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, domin ya amsa tambayoyi game da kalamansa a kan ‘yan bindiga da satar mutane a Arewa.
Wannan dai na zuwa ne, biyo bayan kalaman da malamin ya yi dangane da sace dalibai da malamai sama da 137 da aka yi a Jihar Kaduna kwanan nan.
- Hukumar PSC Ta Sanya 16 Ga Watan Afrilu Don Tantance Lafiyar Masu Neman Aikin Dansanda
- An Kaddamar Da Cibiyar Yada Labarai Ta Dandalin Bo’ao
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce gwamnati ta duba dacewar ta gayyace malamin domin amsa tambayoyi.
A cewarsa, kalaman malamin na bukatar lallai a tattauna da ‘yan bindiga ne ya sanya aka gayyace shi, domin jin ta bakinsa.
Ministan, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, ya bayyana cewa Gumi bai fi karfin doka ba, kuma dole ne a tuhume shi game da kalamansa.
Ministan ya ce: “Gwamnati ba za ta daina yin komai ba don neman bayanan da ake bukata don magance mana matsalolin da suka addabe mu, jami’an tsaro suna yin aiki.
“Sheikh Gumi ko wasu mutane ba su fi karfin doka ba, idan yana da shawarar da ta dace ya bai wa jami’an tsaro ana maraba da ita, amma wasu kalaman ba za a zuba ido a kalle su ba.
“Babu wanda ya fi karfin doka. Kuma ina sane da cewa jami’an tsaro sun gayyace shi (Gumi) domin amsa tambayoyi.
“Duk lokacin da wani zai yi tsokaci game da tsaron kasarmu dole ne a yi bincike, don babu wanda ya fi karfin doka.”