• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Alkaluman Sun Shaida Hasashe Mai Kyau Da Aka Yi Wa Tattalin Arzikin Kasar Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
Alkaluma

A baya bayan nan, manyan ma’aunai uku na tattalin arzikin kasar Sin sun karu tare, abun da ya ja hankalin kasashen waje sosai. A ganin kafofin watsa labaran kasashen waje, ciki har da kamfanin dillancin labarai na Faransa wato AFP, wadannan alkuluman da suka zarce hasashen da aka yi, alamomi ne masu dumi-dumi na karuwar saurin farfadowar tattalin arzikin Sin, lamarin da ba kara wa mutane kwarin gwiwa kadai ya yi ba, har ma da zuba sabon kuzari ga tattalin arzikin duniya.

Idan aka kwatanta da makamancin lokacin a watan da ya gabata, alkaluma masu dumi-dumi da sassan gwamnatin Sin suka bayar a watan Maris na bana sun nuna cewa, ma’aunin kayayyakin da masana’atu ke sayarwa na PMI ya kai kashi 50.8 cikin dari wato karuwar kashi 1.7 cikin dari, kana ma’aunin ayyukan kasuwanci da ba na masana’antun samar da kayayyaki ba, ya kai kaso 53 cikin dari, karuwar kashi 1.6 cikin dari, haka ma hadadden ma’aunin samarwa da fitar da kayayyaki na PMI ya kai kashi 52.7 cikin dari, karuwar kashi 1.8.

Game da wannan, kamfanin dillancin labarai na Bloomberg na Amurka da sauran kafofin watsa labaran kasashen duniya sun bayyana cewa, alkaluman sun nuna makoma mai kyau ta masana’antun samar da kayayyaki na Sin, haka kuma sun nuna cewa tattalin arzkin kasar yana gudana yadda ya kamata..

  • Sin Ta Mai Da Martani Ga Yadda Amurka Ta Gyara Matakin Kayyade Fitar Da Kayayyakin Sassan Laturoni Zuwa Ketare

Me ya sa tattalin arzikin Sin ya samu irin wannan tagomashi? Wani mai binciken harkokin tattalin arziki ya bayyana cewa, ban da karuwar bukatu na cikin gida da tallafin bukatu na waje, an dogara ga manufofin da gwamnatin Sin ta tsara don kyautata yanayin tattalin arziki, da habaka bukatun cikin gida da kuma kiyaye yanayin cinikin waje.

Kazalika, ma’aunin samar da kayayyaki, da ma’aunin sabbin kwangiloli, da kuma ma’aunin cinikin shige da fice, sun yi kyau a watan Maris, wanda ke nufin yanayin tattalin arzikin Sin na kyautatuwa, haka kuma yana tafiya kan hanyar ci gaba lami lafiya. Mai binciken ya kara da cewa, wannan ya nuna saurin karuwar GDPn a rubu’in farkon bana na da kyau, wanda ya aza harsashi ga cimma burin karuwar tattalin arziki na kashi 5 cikin dari a shekarar nan.

LABARAI MASU NASABA

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

Babban mai nazari na cibiyar Brookings, Christopher Thomas, ya bayyana cewa, Sin na kara saurin bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, kuma wannan zai sa sakamakon kirkire-kirkire da aka samu ya kawo alheri ga duk fadin duniya, lamarin da zai kara sabon kuazari ga tattalin arzikin duniya.(Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal
Daga Birnin Sin

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
Daga Birnin Sin

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza
Daga Birnin Sin

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
Next Post
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kaiwa Ofishin Jakadancin Iran Dake Syria

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kaiwa Ofishin Jakadancin Iran Dake Syria

LABARAI MASU NASABA

Alkaluma

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

October 10, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

October 10, 2025
Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi

Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi

October 10, 2025
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

October 10, 2025
Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi

Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi

October 10, 2025
An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.