Babban hafsan tsaron Nijeriya, Christopher Musa, ya ce sarakunan gargajiyar yankin Okuama da ke Jihar Delta, sun taka rawa a kisan da aka yi wa sojoji 17 a jihar.
A ranar 14 ga watan Maris ne, wasu fusatattun matasa suka kai wa dakarun bataliya ta 181 hari, tare da kashe sojoji 17 ciki har da Manjo guda biyu da kuma m Kyaftin guda daya.
An kai wa sojojin harin ne lokacin da suke kokarin kwantar da tashin hankalin da ya kunno kai tsakanin kabilar Okuama da kuma Okoloba a jihar.
Hakan ta sanya rundunar ta ayyana neman wasu sarakuna takwas ruwa a jallo, sakamakon mutuwar manyan sojojin.
Basaraken masarautar Ewu, da ke yankin karamar Ughelli a jihar, Clement Ikolo wanda ya kasance cikin wadanda rundunar ke nema ruwa a jallo, yanzu haka yana tsare a hannun a Abuja.
Sai dai sarakunan gargajiyar sun ce basu da hannu a rikicin yankunan da ya kunno da hakan ya yi sanadin mutuwar wadannan sojoji 17.