Gwamnatin tarayya ta ce ta dukufa wajen ganin ta shawo kan asalin matsalolin da suke addabar bangaren wutar lantarki tare da nemo mafita a kansu.
Ministan wutan lantarki, Adebayo Adelabu shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida jim kadan bayan ganawa da ya yi da wasu masu ruwa da tsakani na jam’iyyar APC a sakateriyar jam’iyyar na Jihar Oyo da ke Oke-Ado a Ibadan.
- Abubuwa 10 Da Ya Kamata A Sani Game Da Sabon Tsarin Biyan Kudin Wutar Lantarki
- Matsanancin Rashin Lantarki Ya Addabi ‘Yan Nijeriya
Ministan ya ce Shugaban kasa, Bola Tinubu ya himmatu wajen kawo gagarumin sauyi a bangaren wutar lantarki.
Ya ce, “Bari na yi amfani da wannan damar na tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa gwamnatin Bola Tinubu a shirye take wajen ganin ta sauya abubuwan da suke faruwa a harkar wutar lantarki, ta canja takun da ke bangaren. Wannan dalilin ne ya sa yanzu muka dukufa wajen shawo kan asalin matsalolin wutar lantarki.
“Muna yin wannan aikin shawo kan dukkanin matsalolin ne tare da yin aikin hadin guiwa da dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren domin nemo mafita, kama daga bangaren samar da gas zuwa tarawa, watsawa da kuma rarraba wutar lantarki hadi da su kansu kwastomomi masu amfani da lantarkin. Akwai abubuwa da dama da muke yi kuma abubuwa za su fara canzawa.”
Ya ce a yanzu ma akwai ci gaba da ake samu a wasu wuraren, amma yanzu ma aka fara samun shawo kan lamura ta yadda ‘yan Nijeriya za su mori lantarki fiye da yadda suke tunani cikin rahusa da kuma inganci a wadace.
Adebayo ya roki ‘yan Nijeriya da su kara hakuri da gwamnatin Tinubu, yana mai cewa halin da ake ciki na wucin gadi ne lamura za su sauya nan ba da jimawa ba.
“Ni kaina na himmatu wajen ganin na shawo kan matsalolin da suke bangaren wutar lantarki, kuma tabbas a kwanan nan ‘yan Nijeriya za su fara rausayawa suna murna da ci gaba da za mu kawo a bangaren,” ya shaida.
Da yake magana kan kokarin gwamnati na shawo kan matsalar karancin mita a Nijeriya, ministan ya ce shugaban kasa ya kafa kwamitin kula da lamuran mita, kuma sun himmatu wajen samar da sama da biliyan 75 domin tabbatar da akalla mita guda miliyan 2 an sanyasu nan da shekaru biyar masu zuwa.