Assalamu Alaikum! Masu karatu barkanmu da sake kasancewa da ku a cikin wannnan shiri, idan ba a manta ba muna bayani ne a kan KURAKURAN IYAYE WAJEN TARBIYYA, inda a makon jiya muka fara tabo batun yadda bai kamata iyaye mata suna bari ana yi wa ‘ya’yansu wasu abubuwa da suka shafi al’aurarsu ba irin su tsarki da wankin ‘inner wares’ wanda ko ga mutane nakusa abin na da illa ballantana na nesa.
A nan zan yi jan hankali gare mu mata mu sani ita ‘ya mace jikinta ba kamar na namiji ba ne, halittarsu ta bambanta wanda bai kamata a ce jinsi daban na taba ta kuma har yana mata tsarki ba, dan za ta iya jin wani yanayi a jikinta da tunanin abin da hankalinsu bai kamata a ce ya kai ba a shekarunsu.
Amma saboda wadannan abubuwan na jikinsu za su iya fara ji. Da wannan nake cewa ya kamata duk abunda ya shafi Mace duk kankantarta a matsayinki na Uwa ki tsaya ki dauke shi ‘serious’ sosai, kar ki ce dan’uwanta ne uwa daya uba daya da sauransu, ba haka abin yake ba.
Wadannan abubuwa suna daga matsalolin da muke fuskanta a wadannan lokuta, ya kamata iyaye mu gane mu kara tsayawa wajen kulawa da tarbiyyar yaranmu mata da maza. Idan mace za ta iya jin wani abu a jikinta da kai tunaninta wani wuri daban, ya kuke gani ga da namiji?. Wankin ‘pants’ ko in ce ‘inners’ sai in ga kamar rashin sanin darajar kanki ne kawai zai sa ba za ki wanke ‘inners’ dinki da na yaranki mata ba ko da ‘yar yarinya ce ba, bare harya zamana kina diba ki ba dan malam wankinsu ko yaranki maza. Ki ba da kayan wanki amma ‘inners’ dinki su ne asalin sirrinki, ta yaya za ki ba almajiri wanki ‘inners’ dinki ko na diyanki, dan Allah mata mu gyara wannan, a cire kiwa da ganda.
Lallai akwai lokacin da ya kamata Uba ya ja ‘yarshi Mace a jiki musamman idan ta soma girma a wannan lokutan kar ya ce komai Uwa ce, ita mace ce da sauransu domin yin hakan kamar ya ba wani katone a waje damar bata mishi ‘ya musamman a irin zamanin da muke ciki.
Wasu iyaye mazan da yayyu Maza ba su san a wata ya kamata a ce sun cire mata kudi ko sun siyo mata abubuwan bukata musamman ‘Pad’ kunzugu, ‘yan kayan kyalekyali da sauransu har sai ka ga wani kato ya soma jan ra’ayinta da ire-iren wadannan abubuwan yana kashe mata kudi da sauransu.
Tun da a gida mahaifi bai da lokacinta sam bare ya san me take ciki me take bukata, haka yayyunta maza sai barazanar shi yayanta ne amma bai taba sanin tana bukatar ‘Pad’ ko wasu abubuwan bukata ba sam ba ruwansa, wani wayar hannunta ma bai san ina ta samo ba.
Iyaye mata na da rauni kan ire-iren abubuwan nan sosai, to kusan a wannan zamanin akan yi sa’a da iyaye Maza marasa lokacin kulawa sam ba su da lokaci sai an yi laifi su yi ihu su wuce shikenan wanda hakan ba zai hana gobe a kuma ba sam, ALLAH ya sa mudace Amin.
A halin yanzu kuma ga wasu shawarwari gare mu a matsayinmu na iyaye kamar haka:
1. Mu guji aikata munanan abubuwa saboda yaranmu na ganin duk abin da muke ba ma boye musu saboda bacin watarana. In za ka bada tarbiya ka ba da me kyau wanda al’umma za su amfana Manzon Allah (SAW) ya yi alfahari da shi, to mu zama nagari.
2. Iyaye su guji yin wasu abubuwa a gaban ‘ya’yansu kamarsu fada wanda an san yau da gobe da kuma aikata Sunnah yayin da ‘ya’yansu ke guri ko farke. Yana da kyau da yaro ya bude baki inda hali a raba shi da dakin iyayen. Domin fadin Manzon Allah ne (SAW) “Narantse da wanda raina ke hannunsa, da namiji zai sadu da matarsa kuma a cikin dakin akwai yaron da yake farke yana ganinsu yana jin kalamansu, da numfashinsu ba zai rabauta ba har abada, idan yarone zai zama mazinaci, idan yarinya ce ta zama Mazinaciya”. Wannan Hadisi yana nuna illar kwana daki daya da yaro wanda ke da wayau, dan haka shi ma yana daga cikin manyan abubuwan da ke lalata tarbiya, iyaye mukiyaye. A nan za mu dasa Aya Allah ya ba mu ikon gyarawa Amin.