Wani rahoton da aka fitar ya nuna cewa, a shekarar bara, adadin sabbin kamfanoni masu zaman kansu dake da karfin jari da aka yiwa rajista a kasar Sin sun karu da guda 56.
Rahoton na alkaluman “Hurun Global Unicorn” na shekarar 2024, wanda aka fitar a jiya Talata, ya ce akwai jimillar irin wadannan kamfanoni 1,453 a duniya baki daya. Kasar Sin na da jimillar 340 a matsayi na biyu a duniya, yayin da Amurka ke matsayi na daya da jimillar 703.
- PLA Ta Gudanar Da Atisayen Hadin Gwiwa A Kan Teku Da Sararin Sama A Tekun Kudancin Kasar Sin
- Ana Fatan Amurka Za Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Bayan Ziyarar Janet L. Yellen A Sin
Nau’in wadannan kamfanoni a kasar Sin dai na gudanar da hada hada ne a fannonin kirkirarriyar basira ko AI, da na kirar sassan na’urorin laturoni na “semiconductors”, da kuma fannin sabbin makamashi.
Jadawalin kamfanonin masu karfin jari na duniya na shekarar 2024, na kunshe da sabbin kamfanonin da ake kafawa bayan shekara ta 2000 a sassan duniya daban daba, wadanda kuma darajar su ta kai a kalla dalar Amurka biliyan daya, kana ba a yi rajistar su a kasuwar hada hadar hannayen jari ba. (Saminu Alhassan)