• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Rabon Hatsi Tan 42,000

by Yusuf Shuaibu
1 year ago
Hatsi

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da rabon hatsin har tan 42,000 gabanin fara bukukuwan karamar sallah.

Ministan yada labarai Mohammed Idris ya bayyana cewa rabon hatsin tan 42,000 yana daga cikin wani bangare na shirye-shiryen gwamnatin tarayya na rage radadin kuncin rayuwa da na tattalin arziki ga daukacin ‘yan Nijeriya.

  • Sin: An Fitar Da Tsarin Tallafin Kudade Domin Bunkasa Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
  • Liu Yuxi Ya Halarci Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kan Sin Da Afirka Karo Na Uku

A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labaran ministan, Suleiman Haruna ya fitar, ya ce ministan ya bayyana hakan ne a wurin kaddamar da rabon kayan abinci ga mabukata a daukacin kasar nan.

Kaddamar da rabon dai ya gudana ne saura kwanaki uku ga bikin karamar sallah, a wani yunkuri na gwamnatin tarayya na rage hauhawar farashin kayayyakin abinci a kasar nan baki daya.

Ministan ya ce Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya damu matuka da yadda kayayyakin abinci suka yi tashin gwauron zabi a Nijeriya, wanda hakan ta sa ya amince da bayar da umurnin raba tan 42,000 na hatsi, wadanda suka hada da gero, dawa, masara da kuma shinkafa tan 60,000.

LABARAI MASU NASABA

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ya ce shirin gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa za ta sake fasalin manufofinta na rage radadin kuncin rayuwa, wanda ba da jumawa za a shawo kan lamarin.

“Gwamnati tana kara kira ga ‘yan Nijeriya su kara ci gaba da hakuri da wannan kuncin rayuwa, mun dauki matakai da za su fitar da ku daga wannan mummunan yanayi. Ba zai gaza jaddada muku cewa wannan yanayin ba zai taba tabbata ba za mu kawo karshensa.”

Ya ce a yanzu haka an samu ragin shigowa da man fetur da kashi 50 duk wata, sannan an samu karuwar darajar naira wanda duk suna cikin shirin sake bunkasa ayyukan ci gaban al’ummar Nijeriya.

“A ‘yan kwanakin da suka gabata, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shiri a bangaren wutar lantarki da nufin bunkasa fannin domin ‘yan Nijeriya su sami ishasshen lantarki.

“Abu mai muhimmanci ga wannan tsarin dai shi ne, Gwamnatin Tinubu ta bayar da kashi 85 na tallafin lantarki ga ‘yan Nijeriya wanda yakan ya tabbatar da kasancewarta gwamnatin dimokuradiyya mai goyon bayan al’umma tare da kara kahi 15 kacal na kudaden wutar lantarkin ga masu yawan samun wutan.

“Ina kira gare ku da ku ci gaba da goyon bayan Gwamnatin Tinubu a daidai lokacin da take aiwatar da tsare-tsareta domin sake fasalin tattalin arzikin kasa,” in ji shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nijeriya
Labarai

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)
Labarai

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Next Post
Babu Wani Shiri Na Kwaso ‘Yan Nijeriya Daga Falasdin Ko Isra’ila –Gwamnatin Tarayya

Jiga-jigan APC Da Ke Tsammanin Samun Mukamin Siyasa A Gwamnatin Tinubu Sun Shiga Rudani

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Hatsi

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.