Jami’an ‘yan sanda farmaki wasu gungun Matasa (Maza) a wajen biki suna shirin yin auren jinsi a Jihar Katsina.
Kamar yadda majiyar Katsina Post ta tabbatar, mutanen sun hadu ne a wani masaukin baki dake cikin garin Katsina a ranar Asabar suna shirye-shiryen yin shagulgulan bikin na su na jinsi kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.
Wasu masu kishi ne, mazauna yankin suka fallasa asirin matasan ta hanyar sanarwa Hukumar tsaro ta ‘yan sandan Jihar.
Yanzu haka dai jami’an yan sandan sun cafke mutane da dama a wurin kuma suna cigaba da bincike domin gano yadda lalatar take.
Auren jinsi laifi ne babba a kundin tsarin mulkin Nijeriya, kuma bashi da mazauni a addini ko al’adar wata kabila a Kasar.