Gidauniyar Ci Gaban Kafofin Watsa Labarai ta Afirka (AMDF), ta taya ‘yan jaridar Afirka murnar zagayowar ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya ta 2024.
Gidauniyar ta jaddada muhimmancin bai wa ‘yan jarida ‘yanci, mutuntawa da kuma riƙon amana.
- WPFD 2024: Aikin Jarida A Yanayi Na Taɓarɓarewar Muhalli
- ‘Gwamnatin Kano Da NNPP Sun Illata Siyasar Ganduje Duk Da Rashin Nasarar’
Wannan na cikin wata sanarwa da manajan kare ‘yancin ‘yan jarida na AMDF, Zhiroh Jatau, ya fitar a ranar Juma’a 3 ga watan Mayu, 2024.
AMDF ta nuna irin muhimmanci da rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen tabbatar da ‘yanci, da riƙon amana.
Taken ranar na bana, “Rawar Da ‘Yan Jarida Ke Takawa A Duniya: Yadda Aikin Jarida Ke Tunkarar Rikicin Muhalli,” ranar ta jaddada rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen bayar da shawarwarin samar da yanayi mai inganci.
Saboda haka gidauniyar ta jaddada muhimmancin fallasa kamfanoni da ƙungiyoyin da ke lalata albarkatun da ke doron ƙasa.
Wasu daga cikin matsalolin sun haɗa da sauyin yanayi, gurɓatar yanayi, da lalacewar hallitu, wanda gidauniyar ta bukaci ‘yan jarida su taka rawa wajen bayar da shawarwarin da za su kare muhalli daga gurɓacewa.
Gidauniyar ta ja hankali kan yiwuwar samun cin zarafin ‘yan jarida a ƙasashe irin su Ghana, Namibiya, Nijeriya, da Cape Verde, inda ake tsare ‘yan jarida, tare da kai wa kafafen watsa labarai samame sakamakon ayyukan da suke gudanarwa.
Abin takaici, yawancin ‘yan jaridar da ke bibiyar al’amuran da suka shafi cin hanci da rashawa a Afirka na fuskantar cin zarafi ta hanyar ɗauri da yi wa rayuwarsu barazana.
Saboda haka, AMDF ta yi kira ga hukumomin tsaro a Afrika da su ɗauki gaɓaren kare ‘yan jarida, tare da samar musu da yanayin da za su gudanar da ayyukansu cikin salama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp