A daren jiya Lahadi ne gobara ta kone wani bangare na gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da ke unguwar Mundubawa, inda ta ci dakunan matarsa ta uku, Halima Shekarau.
Kawo yanzu dai ba a iya gano musabbabin tashin gobarar da ta tashi a dakin dafa abinci na gidan ba a daren Lahadi.
- Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Mutane 12 Da Dukiyar Miliyan 130 A Kano
- Gobarar Dare Ta Kone Shaguna 40 A Kano
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, mai bai wa Malam Shekarau shawara kan harkokin yada labarai, Dokta Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta tashi ne da yammacin ranar Lahadin da ta gabata daga dakin girki na cikin gidan.
Ya ce, “Mun gode wa Allah da ya takaita gobarar ta shafi iya daya daga cikin dakin Malam Ibrahim Shekarau ne kawai, kuma tuni jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka yi nasarar kashe gobarar.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, da aka tuntube shi, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ki yin karin bayani kan musabbabin tashin gobarar, inda ya ce ana ci gaba da kai dauki gidan.
Ya kara da cewa “Har yanzu muna gidan kuma kun san ba zan iya cewa komai ba a yanzu saboda muna kokarin ganin cewa gobarar ba ta bazu zuwa wasu wurare gidan ba.” A cewarsa.