Wata kotu da ke zamanta a garin Jos ta ta amince da rokon wata matar aure, Rhoda Jonathan da ke neman a raba aurenta bisa hujjar cewa mijinta, Dakogol ya gudu ya barta tare da budurwarsa.
Jonathan a takardar neman a raba auren nata, ta yi zargin cewa Dakogol na yawan zaginta kuma ya kasa biyan bukatun iyalinsa.
- Yawan Tashar Sadarwa Ta 5G Da Sin Ta Gina Ya Kai Kusan Miliyan 2
- Buhari Ya Bai Wa Ministan Ilimi Mako 2 Don Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU
Alkalan da suka jagoranci shari’ar, Sadiq Adamu da Hyacenth Dolnanan, a wajen amincewa da rokon Jonathan da ta gabatar, sun ce; “duk kokarin sulhunta ma’auratan ya ci tura”.
Alkalan sun umarci mai kara da wanda ake kara da su rabu da juna kawai.
Sai dai kotun ta umurci Dakogol da ya rika bayar da kudin kula da ‘ya’yansa duk wata.
Tun da fari, Jonathan ta roki kotu da ta raba aurensu, inda ta ce mijin nata da suke tare tsawon shekaru 20, ya kasa kula da ‘ya’yansu uku.
“Kafin ya gudu, watanni hudu da suka gabata, muna yawan samun sabani, har ta kai ga ya daina sauke hakkinsa a matsayin mijina .
“Na gaji kuma ina so in ci gaba da rayuwata,” in ji ta.