Babban bankin Nijeriya (CBN), ya umarci bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara cire harajin kashi 0.5 daga asusun kwastomomi domin tsaron yanar gizo.
CBN ya ce za a rika cire kudin ne da zarar kwastomomi sun tura kudi daga asusunsu ta hanyar amfani da yanar gizo.
- Dillalai Sun Yi Barazanar Daina Kai Tumatir Jihar Legas
- Gwamnatin Nijeriya Na Ƙoƙari Wajen Daƙile Hauhawar Farashin Magunguna
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun daraktan kula da tsarin biyan kudi, Chibuzor Efobi da Haruna Mustafa, daraktan tsare-tsare na kudi a ranar Litinin.
“Saboda haka ana bukatar dukkanin bankuna, cibiyoyin hada-hadar kudi su aiwatar da wannan doka; za a yi amfani da harajin ne a duk lokacin da kwastomomi suka tura kudi ta yanar gizo.”
Babban bankin ya bayar da umarnin ne ga bankunan kasuwanci, manyan ‘yan kasuwa da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi.
CBN ya ce wannan umarnin zai fara aiki nan da makonni biyu masu zuwa, kuma za ake amfani da kudin wajen tsaron yanar gizo don yaki da masu datsar bayanan mutane a yanar gizo.
CBN ya ce cirewa da tattara harajin kudin tsaron ya biyo bayan aiwatar da dokar aikata laifuffuka a yanar gizo ta 2024 da aka sabunta.
CBN ya ce za a mika kudaden ne ga asusun tsaron yanar gizo na kasa, wanda ofishin hukumar NSA zai gudanar.
Babban bankin ya ce rashin cire harajin wani laifi ne da ya saba da sashe na 44 (8) da ka iya jawo tarar sama da kashi 2 na ribar shekara da bankuna ko cibiyoyin hada-hadar kudi suka samu.